Inna Lillahi: Yariman Saudiyya Talal bin Abdulaziz Ya Rasu, Tinubu Ya Mika Sakon Ta’aziyya

Inna Lillahi: Yariman Saudiyya Talal bin Abdulaziz Ya Rasu, Tinubu Ya Mika Sakon Ta’aziyya

  • Allah ya yi wa yariman kasar Saudiyya Talal bin Abdulaziz rasuwa, an gudanar da jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar
  • Yarima Talal wanda dan uwa ne ga Sarki Salman na Saudiyya, ya rasu yana da shekaru 87, kuma ya kasance da ne ga Sarkin Saudiyya na farko, Abdulaziz
  • Shugaban kasar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Sarki Salman da zuriyar masarautar Saudiyya kan wannan rashi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga Sarki Salma na kasar Saudiyya da kuma masarautar kasar kan mutuwar Yarima Talal bin Abdulaziz bin Bandar Al Saud.

Sakon ta'aziyyar na kunshe ne a cikin wata wasika da Tinubu ya aika wa Saudiyya a ranar Asabar ta hannun mai bashi shawara ta fuskar watsa labarai, Ajuri Ngelale.

Yarima Talal bin Abdulaziz ya riga mu gidan gaskiya
Allah ya yi wa yariman Sadiyya, Talal bin Abdulaziz rasuwa sakamakon hatsarin jirgin sama, an yi jana'izarsa a Riyadh. Hoto: Arab News
Asali: UGC

Jaridar PM News ta ruwaito cewa Talal bin Abdulaziz bin Bandar Al Saud, mai shekaru 62 ya rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a ranar Alhamis 7 ga watan Disamba.

Kasar Saudiyya ta sanar da rasuwar Yarima Al Saud a cikin wata sanarwa, inda za a gudanar da jana'izarsa a masallacin Imam Turki bin Abdullah a birnin Riyadh, The Nation ta ruwaito.

An yi jana'izar Yarima Talal a Riyadh

Jaridar Saudiyya SPA ta wallafa wasu hotunan jana'izar mamacin, inda aka ga Yarima Alwaleed na dauke da gawar mahaifinsa da taimakon dan uwansa Yarima Khalid.

Akwai kuma jakadan Saudiyya a Burtaniya na masarautar Yarima Mohammed bin Nawwad da Yarima Muqrin bin Abdulziz a mahalarta jana'izar.

Har ila yau, SPA ta wallafa hotunan da suka nuna Sarki Salman ya na jagorantar addu'ar janazar, inda iyalai da mambobin masarautar suka kewaye gawar, ciki har da Yarima Turki bin Faisal, tsohon jakadan Saudiyya a Washington da Landan.

Janar Kure da ya jagoranci murkushe Maitatsine a Kano ya rasu

A wani labarin na daban, Legit ta ruwaito rasuwar Janar Yerima Kure, tsohon kwamandan rundunar soji da ya jagoranci murkushe Maitatsine a Kano.

Janar Kure ya rasu yana da shekaru 84.

Asali: Legit.ng

Online view pixel