Kwanaki 6 da Dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu Zai Lula Kasar Larabawa a Gobe

Kwanaki 6 da Dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu Zai Lula Kasar Larabawa a Gobe

  • Fadar Shugaban kasa ta bada sanarwa a yau cewa Bola Tinubu zai tafi kasar waje domin halartar taro
  • Bola Ahmed Tinubu ya na cikin wadanda za su yi jawabi a zaman COP28 da za ayi wannan karo a Dubai
  • Majalisar dinkin Duniya ta shirya taron da za a gudanar a kasar UAE a game da sha’anin sauyin yanayi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Larabar nan ne Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya zuwa birnin Dubai a kasar tarayyar Larabawa (UAE).

Ajuri Ngelale ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar daga fadar shugaban kasa a Abuja.

Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen yada labarai da kuma hulda da jama’a ya ce Bola Tinubu zai je wajen taron COP28.

Kara karanta wannan

Labari Da Dumi Dumi: Tinubu Zai Gabatarwa 'Yan Majalisa Kasafin Kudin Farko a Mulkinsa

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu zai je Dubai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

COP28: Bola Tinubu zai tafi Dubai

Majalisar dinkin duniya ta shirya babban taron domin tattaunawa a kan abubuwan da su ka shafi sauyin yanayi a Duniya.

Bola Tinubu wanda bai dade da dawowa daga ketare ba zai yi jawabin da ya shafi matsayar Najeriya kan batutuwa da-dama.

Fa'idar zuwan Tinubu ga Najeriya

Ngelale ya ce Tinubu zai yi amfani da damar wajen neman taimako ga kananan kasashen duniya masu kokarin tasowa a yanzu.

Tinubu zai tunawa manyan kasashe alkawarin da su ka yi na bada gudumuwar $100bn domin magance matsalolin sauyin yanayi.

Daily Trust ta ce Mai girma shugaban Najeriya zai tattauna a kan yunkurin da kasarsa ta ke yi na kawo kalubalen da ake fuskanta.

Yause za ayi taron COP28?

Jawabin ya ce za ayi taron ne a ranakun Juma’a da Asabar da su ka fado a matsayin 1 da 2 ga watan Disamban nan da za a shiga.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ake shirin tsige Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Mai magana da yawun shugabankasar ya ce tawagar Najeriya za ta dage domin kulla dangantaka da sauran kasashe na duniya.

A karshe, da zarar an kammala taron, jirgin shugaban kasa zai dawo Najeriya.

Tinubu ya dawo daga Jamus

Mako da su ka wuce kenan aka ji Bola Tinubu da tawagarsa sun dawo Najeriya bayan halartar wani taro da aka shirya a kasar Jamus.

Wannan karo ana sa ran kasashen da su ka shiga wannan yarjejeniya za su tura shugabanninsu da wakilai zuwa taron COP28.

Asali: Legit.ng

Online view pixel