Tashin hankali yayin da ango ya kashe amarya da surukarsa a ranar aurensu

Tashin hankali yayin da ango ya kashe amarya da surukarsa a ranar aurensu

  • Dokin zuciya ya ja wani ango ya kashe amaryarsa, kanwarta da surukarsa a ranar aurensu a lardin Arewa maso Yammacin kasar Thailand
  • An ruwaito cewa ango da amaryar sun dan samu sabani har ta kai su ga cacar baki, lamarin da ya harzuka angon ya dauko bindiga ya kashe mutum hudu
  • Angon ya kasance fitaccen dan wasan tseren ruwa ne, wanda ya lashe kambunan girmamawa da dama, kuma tsohon sojan Thai ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Thailand - Wani fitaccen dan wasan guragu, Chaturong Suksuk, ya kashe amaryarsa mai suna Kanchana Pachunthuek, surukarsa da kanwarta a ranar daurin aurensu a Arewa maso Yammacin kasar Thailand, a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari wasu garuruwa a arewa, sun tafka barna da kashe mutum 20

Rahotanni sun bayyana cewa harsashe ya samu wasu baki biyu inda aka garzaya da su asibiti, sai dai daga daga cikinsu ya bakunci lahira.

Thailand/Ango da amarya
Suksuk ya aikata wannan danyen aikin ne bayan da dokin zuciya ya haushi kan bambancin shekaru da nakasarsa. Hoto: @Thaiexerminer
Asali: Twitter

Suksuk, wanda tsohon jami'in soji ne, an ruwaito cewa ya bar wajen taron bikin sannan ya dawo dauke da bindiga, wacce ya yi amfani da ita wajen kashe mutane hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cacar baki angon ya dauko bindiga ya fara harbi - Yan sanda

Dan wasan tseren ruwa na guragu mai shekaru 29 ya samu kambun girmama har sau biyu a gasar ASEAN Para Games ta 2022 da aka gudanar a Indonesia da Cambodia, Daily Trust ta ruwaito.

Wani rahotan jaridar Daily Mail ya nuna cewa Suksuk ya aikata wannan danyen aikin ne bayan da dokin zuciya ya haushi kan bambancin shekaru da nakasarsa.

"Sun san samu sabani kan wani batu da ya shafe su, daga nan aka Chaturong ya je mota ya dauko bindiga, ya fara harbi."

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun kai samame maɓoyar yan bindiga a garuruwa 6, da yawa sun sheka lahira

Cewar Matichon Wongbaokul, jami'in dan sanda daga Arewa maso Gabashin lardin Nakhon Rathasima.

Shi tsohon jami'in sojan Thai ne, ya rasa kafarsa ta dama yayin wani rangadi a bodar kasar.

Gobara ta babbake babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi

A wani labarin, wata gobara da ta tashi a Asubahin ranar Litinin, ta jawo asarar miliyoyin naira a wani bangare na babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi, Legit Hausa ta ruwaito.

Gobarar ta lakume shaguna masu tarin yawa, yayin da ta bar 'yan kasuwa da mazauna yankin cikin tashin hankali, babu wanda ya iya shawo kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel