Kasashen Duniya
Sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Faye ya kawo ziyara Najeriya yayin da ya sanya labule da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke birnin Abuja.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya magantu yayin da kamfanin jiragen Emirates ya sanar da cewa zai dawo jigilar fasinjoji a Nigeria a watan Oktoba.
Sherif Lawal ya fafata ne a filin dambe na J Hackney Leisure inda ya ji rauni a zagaye na hudu a karawarsa da Malam Varela; an tabbatar da mutuwarsa a asibiti.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby murnan lashe zabe inda ya yi masa alkawarin ba shi dukkan goyon baya a kasar.
Hukumar hana fasa kwauri ta ce ta damke lita 12,435 na man fetur wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 10.8 a hanyar Cameroon. An kuma kama jarka 61 a hanyar Benin.
A cikin shekara 1, Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci kasashe 14 a tafiye-tafiye 20 da ya yi zuwa kasashen waje. Mun tattara jerin ƙasashen da dalilin tafiye-tafiye.
Kungiyar ALDRAP ta maka mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da sauran sanatoci 39 kan kasancewa mambobin majalisu 2 mabambanta.
'Yan jarida na taka rawa wajen samar da bayanai da rahotanni ga al'umma. Sai dai akwai kasashen da ba su da cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Akalla ma'aikata 200 ne ake fargabar za su rasa aiki a yayin da babban kamfanin kimiya na kasar Amurka, Microsoft, ya fara shirye-shiryen rufe ofishinsa na Najeriya.
Kasashen Duniya
Samu kari