'Dan Wasan Damben Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Matacce a Tsakiyar Fili

'Dan Wasan Damben Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Matacce a Tsakiyar Fili

  • Dan damben Najeriya da ke zaune a birnin Landan, Sherif Lawal ya mutu bayan da ya fadi ana tsakiyar fafata dambe a ranar Lahadi
  • Dan wasan Portugal, Malam Varela ne ya doke Lawan mai shekaru 29 a zagaye na hudu a filin dambe na Harrow Leisure Centre
  • Lawal dai ya samu kulawa daga ma’aikatan jinya a filin damben kuma an garyaza da shi asibiti amma daga baya ya mutu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

London - An jefa duniyar 'yan dambe cikin jimami bayan rasuwar dan damben nan na Najeriya, Sherif Lawal, wanda ke zaune a birnin Landan.

Dan damben Najeriya mazaunin London ya mutu a filin wasa
Likitoci sun tabbatar da mutuwar dan damben Najeriya mazaunin London. Hoto: Hill Street Studios
Asali: Getty Images

Matashin mai shekaru 29 ya rasa ransa bayan ya yanke jiki ya fadi ana tsakiyar fafatawa da shi a babban wasansa na farko a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

An yi dambe tsakanin Lawal da Varela

Lawal ya kara da Malam Varela a fafatawar zagaye shida da aka gudanar a filin wasan dambe na Harrow Leisure Centre, kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa an gwabza fadan har zuwa mataki na hudu, inda Lawal ya samu rauni bayan naushin da ya sha wanda ya sa shi yanke jiki ya fadi.

Kocin Sherif, CJ Hussein, ya garzaya domin kai masa dauki, yayin da kwararrun likitoci, ciki har da likitocin filin damben suka yi kokarin ceton rayuwar Sherif ta hanyar amfani da CPR da sauran dabaru.

Hukumar dambe ta Birtaniya ta magantu

Kafar labarai ta Sky Sport ta ruwaito cewa an kira motar daukar marasa lafiya wadda ta dauki Lawal, zuwa wani asibiti da ke kusa, inda aka tabbatar da mutuwar matashin.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja

Hukumar kula da dambe ta Birtaniya, bisa jagorancin babban sakatare, Robert Smith, ta bayyana kaduwarta sosai kan mutuwar Lawal, tare da mika sakon ta'aziyyarta.

"Yanzu muna kan tattara dukkanin rahotanni daga jami'ai, likitoci, da ma'aikatan jinya domin ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru."

- Robert Smith.

Fafatawar Lawal ita ce ta farko a wannan maraice kuma sanarwar mutuwarsa ta sa aka soke sauran wasannin.

Dan damben Imo ya mutu a filin wasa

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa, wani dan dambe da ke wakiltar jihar Imo a gasar wasanni ta kasa ya mutu a a jihar Delta.

An ruwaito ce dan damben mai suna Chukwuemeka Igboanugo ya mutu ne a cikin filin wasan damben a lokacin da yake fafatawa da abokin karawarsa Prince Gaby Amagor na Anambra.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel