Ba a Gama da Matsalar Gida Ba, Tinubu Ya Yi Alkawari Ga Shugaban Chadi, Deby

Ba a Gama da Matsalar Gida Ba, Tinubu Ya Yi Alkawari Ga Shugaban Chadi, Deby

  • Yayin aka gudanar da zaben a kasar Chadi, Shugaba Bola Tinubu ya taya shugaban murnan lashe zabe
  • Tinubu ya sha alwashin ba Janar Maganar Deby dukkan goyon baya da ya ke bukata da kuma hadin kai
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya taya shugaban kasar Chadi, Janar Mahamat Deby murnan lashe zaben da aka gudanar.

Tinubu ya taya Janar Deby murna inda ya yi alkawarin ba shi dukkan goyon baya da ya ke bukata yayin mulkinsa a Chadi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya, ya dakakar da tsarin biyan harajin 0.5% da CBN ya kawo

Tinubu ya taya sabon shugaban kasar Chadi, Deby murnan lashe zabe
Bola Tinubu ya yi alkawarin taimakawa sabon shugaban kasar Chadi, Janar Mahamat Deby. Hoto: Fayez Nureldine, Anadolu.
Asali: Getty Images

Tinubu ya yabawa zaben kasar Chadi

Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale da aka yada a kafofin sadarwa..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan zaɓe ya kara tabbatar da himmatuwar gwamnatin Chadi wurin gudanar da shugabanci na gari a tsarin dimukradiyya.

Har ila yau, Tinubu ya ba Deby tabbacin goyon baya wurin inganta tsaro da zaman lafiya da kuma ci gaba a tsakanin kasashen.

Yaushe Deby ya hau mulkin kasar Chadi?

Wannan na zuwa ne bayan Mahamat Deby ya ɗare kan kujerar mulkin kasar a 2021 bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno.

Itno wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 30 ya mutu ne yayin arangama da 'yan tawaye a kasar a ranar 20 ga watan Afrilun 2021.

Wannan nasara ta Janar Mahamat ta tabbatar da cewa iyalan Deby za su gaba da mulki fiye da shekaru 30 a kasar da ke yaren Faransanci.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Tinubu ya dakatar da harajin CBN

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan sabon harajin da Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo.

Tinubu ya dakatar da ƙaƙaba tsarin ga 'yan Najeriya inda ya ce bai kamata ba wannan lokaci da ake cikin matsi a kasar.

Wannan ya biyo bayan kawo tsarin biyan harajin 0.5% kan masu tura kudi zuwa bankuna domin tsaron yanar gizo a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.