Jihar Kaduna
Shehu Sani, tsohon sanata na Kaduna ya yi kira ga yan Najeriya su rika yi wa yan uwansu maza da mata masu fama da lalurar asthma addu'a yanzu da hunturu ya shigo.
Kotun daukaka kara ta sanya ranar yanke hukunci kan zaben jihar Kaduna inda ta sanya gobe Juma'a 24 ga watan Nuwamba tsakanin Gwamna Uba Sani da Ashiru Kudan.
Gine-gine 644 aka tabbatar da za su je kasa saboda an sabawa doka a Legas. Akwai gidaje sama da 700 da rushe-rushen zai shafa, hukuma ba za ta ruguza su kaf ba.
Dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu miyagun mutane masu ba yan bindiga bayanai da siyo musu kayayyaki domin gudanar da ayyukansu a jihar Kaduna.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dauki mataki kan wasu kansiloli guda takwas da suka tsige shugaban majalisar karamar hukumar Kagarko, dakatarwar ta din-din-din.
Rundunar Operation Safe Haven ta bayyana cewa sojoji sun yi ajalin wani hatsabibin ɗan bindiga da wasu yan ta'adda 6 duk a ƙaramar hukumar Zangon Kataf.
Kotun koli ta sanya 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar amfani da tsaffin takardun kudade wanda ake ta cece-kuce a kansu.
Magidancin ya shaidawa kotun cewa yana dukan matar da yaran ne kawai idan suka aikata laifi, kuma yana yin hakan don gyara masu tarbiya. Alkalin ya ba shi shawara.
Rundunar sojin ta kai hare-haren ne bayan samun wasu rahotannnin sirri na cewa dan ta'addan mai suna Boderi da mambobinsa na zaune a Tsauni Doka.
Jihar Kaduna
Samu kari