Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata Yan Najeriya Su Yi Addu'a a Lokacin Hunturu

Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata Yan Najeriya Su Yi Addu'a a Lokacin Hunturu

  • Sanata Shehu Sani ya bukaci a taimakawa yan Najeriya da ke fama da lalurar asthma yayin lokacin hunturu
  • Tsohon dan majalisan tarayyar ya yi kira ga yan Najeriya su taya yan uwansu maza da mata da ke fama da lalurar asthma da addu'a
  • A cewar Sani, a halin yanzu ana sayar da inhaler kan kudi N40,000 (naira dubu arba'in) a kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Tsohon Sanata na Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya koka kan tsadar maganin shaka na inhaler da masu fama da lalurar asthma ke amfani da shi.

Ya ce a halin yanzu ana sayar da inhaler kimanin N40,000 (naira dubu arba'in) a Najeriya.

Shehu Sani ya yi kira ga yan Najeriya su yi wa masu asthma addu'a
Shehu Sani ya ce masu lalurar asthma na bukatar addu'a a lokacin hunturu. Hoto: Shehu Sani
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamna ya tona gaskiyar halin da Buhari Ya damkawa Tinubu tattalin arzikin Najeriya

Sani ya yi kira ga yan Najeriya su rika yi wa sauran yan uwansu yan kasa maza da mata da ke fama da lalurar asthma addu'a a wannan yanayi na hunturu.

Tsohon na majalisar na tarayya ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (tsohuwar Twitter) @ShehuSani.

Ya rubuta:

"Yanzu inhaler ta kai N40k. Iskar hunturu ya zo. Ku yi addu'a ga yan uwanmu maza da mata masu fama da lalurar asthma."

Yan Najeriya sun yi martani

@jidifeanyi

Gwamnati na iya saka wannan maganin a rukunin magunguna masu muhimmanci kamar rigakafin cutar shan inna da sauransu.

@MichealOyewole_

Allah ya taimake su ya karfafa su
Yayin da Cif Bola ya ke kokarin shiga Kundin Tarihi na Guiness, kasar na sake tsindumawa cikin wahala da talauci.

@GabrielTari_

Wannan abin bakin ciki ne.
Ina musu addu'ar samun lafiya
Kuma ya kamata gwamnati ta dauki wani mataki kan masu fama da lalurar asthma.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

@anuforo

"Lokaci ne mai wahala sosai yanzu a Najeriya... Tattalin arzikin na shake kowa. Abin takaici, mutane da dama basu son magana kan abin. Duk kasar da bata da kiwon lafiya mai kyau ba ta da tattalin arziki, an ce "ma'aikaci mai lafiya ya kan gaggauta aiki."

@TawaseOmotola1

"APC ta jefa yan uwa maza da mata masu asthma cikin mawuyacin hali yanzu, Allah ya taimake su yayin wannan yanayin hunturun."

@Iselema

"Ba damuwa, wannan shine sakamakon barin Najeriya da GSK ya yi."

Sani Ya Magantu Bayan LP Ta Bukaci Yan Majalisunta Ka da Su Karbi Motoccin N160m

A wani rahoton, Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya mayar da martani bayan shugaban jam'iyyar LP na ƙasa, Julius Abure, ya yi tir da motocin N160m kirar SUV da za a ba kowane daga cikin ƴan majalisar wakilai 360.

Yayin da ya bukaci ƴan majalisar jam'iyyarsa da su yi watsi da kyaututtukan, Abure ya bayyana matakin a matsayin kololuwar rashin hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel