Majalisar Dokoki Na Jihar Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Bayyana Dalili

Majalisar Dokoki Na Jihar Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Bayyana Dalili

  • Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dauki mataki kan wasu kansiloli guda takwas da suka tsige shugaban majalisar karamar hukumar Kagarko
  • Majalisar dokokin ta kuma karbe ragamar ayyukan majalisar karamar hukumar, har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan Nasara Rabo
  • A ranar 2 ga Nuwamba, 2023, kansilolin takwas suka tsige shugaban majalisar karamar hukumar yayin da ake bincikensa kan zargin karkatar da kudade

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta karbe ragamar ayyukan majalisar karamar hukumar Kagarko sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a karamar hukumar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, majalisar dokokin jihar ta dakatar da kansiloli takwas daga karamar hukumar, dakatawar din-din-din.

Kara karanta wannan

Yanzu: An samu sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa a Filato

Zaman majalisar dokoki ta jihar Kaduna
Majalisar dokokin ta dakatar da kansiloli takwas daga karamar hukumar, dakatawar din-din-din. Hoto: @Kadlegislature
Asali: Twitter

Kansiloli takwas da abin ya shafa sun hada da Danjuma Padalo, gundumar Iddah; Adamu Abdulaziz, Kagarko South Ward; Livinus Makama, Aribi Ward; da Samson Hazo, gundumar Katugal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa majalisar ta dakatar da kansilolin

Sauran sun hada da, Amos Egoh, gundumar Kushe; Idris Abubakar, gundumar Jere ta Arewa; Zakaria Musa, gundumar Kukui; da Rabo Musa, gundumar Kurmin Jibrin, rahoton Daily Post.

Jaridar The Punch ta ruwaito majiyoyinta na cewa dakatarwar da aka yi wa kansilolin ba zai rasa nasaba da tsige shugaban majalisar karamar hukumar Nasara Rabo ba bisa ka’ida ba, da kuma saba wa aikin ofisoshinsu.

A ranar 2 ga Nuwamba, 2023, kansilolin gundumomi takwas suka tsige shugaban majalisar a yayin da kwamitin wucin gadi na majalisar ta 10 ke gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa shugaban.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista na PDP ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa

Majalisar Kaduna ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 3

A wani labari makamancin wannan, majalisar jihar Kaduna, ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku a jihar, bisa zargin bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, kamar yadda dokokin jihar ta Kaduna suka tanada.

An bayyana sanarwar dakatarwar tasu a zaman majalisar na ranar Talata, 25 ga watan Yuli kamar yadda Legit Hausa ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel