'Muna Shirin Raka Sarki Ado Bayero Fadarsa a Kofar Kudu,' Tsohon Kwamishina

'Muna Shirin Raka Sarki Ado Bayero Fadarsa a Kofar Kudu,' Tsohon Kwamishina

  • Tsohon kwamishina a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa suna shirin raka Aminu Ado Bayero fadar kofar kudu inda Sarki Sunusi ke zaune
  • A sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook, Mu’azu Magaji ya ce tuni suka shirya tsaf, amma sarkin ya basu umarnin su dan jira har sai jami'an tsaro sun kammala aiki
  • Kano dai ta rikice yayin da tawagar jami’an tsaro daga Abuja suka shigo da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero duk da nadin sabon sarki Malam Muhammadu Sunusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Tsohon kwamishina a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa ana ta shirye-shiryen raka sarki Aminu Ado Bayero fadarsa dake kofar kudu.

Kara karanta wannan

Manyan jami'an tsaro sun yi watsi da Gwamna, sun isa ƙaramar fadar sarkin Kano

Yanzu haka sabon sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II na zaune a fadar ta kofar kudu yana karbar gaisuwa da mubaya daga masoyansa.

Muaz Magaji
Tsohon kwamishinan Ganduje ya ce suna shirin raka Sarki Aminu Bayero fadar kofar kudu Hoto: Mu'az Magaji
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa shima Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa, Aminu AbdulSalam Gwarzo da wasu kusoshin gwamnati na fadar, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon Mu’azu Magaji a facebook

A sakon da Mu’azu magaji ya wallafa ta shafinsa na facebook, ya bayyana cewa a shirye suke su raka Aminu Ado Bayero fadar ta kofar kudu.

A jerin sakonnin da ya wallafa a shafin yau Asabar, ya ce sarki Aminu ya basu hakuri su bari sai jami’an tsaro sun kammala aikinsu.

Rikici ya kunno kai a jihar Kano tun bayan amincewa da dokar rushe masarautun Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi biyayya ga kotu, 'har yanzu aminu ado bayero ne sarkin Kano'

Jami'an tsaro sun mamaye Kano

A baya mun kawo muku labari cewa jami'an tsaron kasar nan sun mamaye gidan gwamnatin Kano yayin da gwamna Abba kabir Yusuf ke fadar sarki Muhammadu Sunusi II.

An gano cewa babban mai tsaron gwamna Abba abir Yusuf na cikin mawuyacin hali domin fuskarsa a turbune yake cike da damuwa yayin da ake zaman dar-dar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel