Rikicin Sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf Ya Yi Shaguɓe Ga Aminu Ado Bayero

Rikicin Sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf Ya Yi Shaguɓe Ga Aminu Ado Bayero

  • Yayin da ake takaddama kan kujerar sarautar Kano, dan Sarki Sanusi II ya yi martani ga Aminu Ado Bayero
  • Ashraf Sanusi Lamido ya ce babu Sarki a Nasarawa tun da fadar na karkashin masarautar Kano ne gaba daya
  • Wannan martani na Ashraf na zuwa ne bayan tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya shigo jihar Kano da safiyar yau Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi martani bayan Aminu Ado Bayero ya sauka a fadar Nasarawa.

Ashraf Sanusi Lamido ya bayyana cewa masarautar Nasarawa tana karkashin ta Kano ne kamar yadda kowa ya sani.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sanya labule da Sanusi II, shugabannin tsaro a Kano, bayanai sun fito

Dan Sanusi II ya soki Aminu Ado kan shiga fadar Nasarawa
Rikicin sarautar Kano ya dauki sabon salo tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Aminu Ado Bayero.
Asali: Twitter

Dan Sanusi II ya soki Aminu Ado

Ɗan Sarkin ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Asabar 25 ga watan Mayu kan dambarwar da ke faruwa..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martani nashi na zuwa ne bayan mahaifinsa, Muhammadu Sanusi II ya dauki lemar sarauta wanda ke tabbatar da mayar da shi karagar mulki.

Hakan ya biyo bayan dawowar tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero jihar da asubahin yau Asabar 25 ga watan Mayu.

Ashraf ya ce:

"Fadar Sarkin Nasarawa na karkashin masarautar Kano ne, babu Sarki a Nasarawa."

Aminu Ado ya shigo Kano

Tsohon sarkin ya samu tarba daga dubban matasa a jihar inda suke ta wake-wake da nuna goyon bayansi tare da addu'o'i.

Daga bisani, Gwamna Abba Kabir ya umarci cafke tsohon sarkin da zarar an gano shi saboda zargin neman ta da tarzoma a jihar.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

Sai dai rundunar yan sanda ta yi fatali da umarnin inda ta tabbatar cewa za ta bi umarnin kotu da ta haramta matakin tube sarkin.

Ribadu ya musanta hannu a rikicin Kano

A wani labarin, kun ji cewa mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano.

Ribadu ya musanta hannu a cikin zargin da ake yi kansa cewa yana kokarin dawo da Aminu Ado Bayero kan karaga a Kano.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kano ta zargi Ribadu da daukar nauyin Aminu Ado Bayero zuwa jihar da safiyar yau Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel