Sanusi II Ya Bayyana Rawar da Tinubu Ya Taka Wajen Dawo da Shi Kan Sarautar Kano

Sanusi II Ya Bayyana Rawar da Tinubu Ya Taka Wajen Dawo da Shi Kan Sarautar Kano

  • Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai yi katsalandan ba wajen dawo da shi kan sarautar Kano
  • Sanusi II ya bayyana komawarsa kan sarauta a matsayin gyara wani rashin adalci da aka yi wa al'umma da al'adun jihar Kano
  • Ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu kan yadda ya ƙi tsoma baki a lamarin duk da matsin lambar da aka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Muhammadu Sanusi II ya ce Shugaba Bola Tinubu bai yi katsalandan ba wajen mayar da shi Sarkin Kano. 

A ranar Alhamis ne Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sanar da mayar da Sanusi II kan sarautar Kano bayan ya rattaɓa hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Sanusi II ya yi magana kan sarautar Kano
Sanusi II ya ce Tinubu bai yi katsalandan wajen dawo da shi kan sarauta ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace rawa Tinubu ya taka kan dawo da Sanusi II

Sanusi II ya ce Tinubu ya fahimci cewa abin da yake faruwa a Kano al'amari ne na cikin gida kuma ya bijirewa duk wani matsin lamba domin ya yi katsalandan a ciki.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara da cewa ba a ba shi damar kare kansa ba bayan da aka tsige shi kan “zarge-zargen da ba su da tushe".

Ya bayyana komawarsa kan karagar mulki a matsayin gyara rashin adalcin da aka yi wa al’umma da al’adar Kano.

"Kamar yadda kuka sani an naɗa ni Sarkin Kano na 14 a watan Yunin 2014 kuma yanzu an sake nada ni a matsayin Sarkin Kano."

Kara karanta wannan

Abin da Sanusi II ya gayawa shugabannin tsaro yayin ganawarsu a Kano

"Muna godiya ga Allah da a yau masarautar ta sake haɗewa, an haɗa jama’arta wuri guda, an gyara wani zalunci domin kamar yadda kuka sani an tsige ni ne bisa zargin rashin biyayya da har yanzu ba a bayyana shi ba."
"Ina so miƙa godiyata ga Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ba tare da rashin tsoma bakinsa kan al'amarin da suka shafi jihar ba, da dawo da ni kan sarauta bai yiwuwa ba."
"Shugaban ƙasan ya nuna cewa shi mai mutunta kundin tsarin mulki ne, ya yarda cewa wannan lamarin abin da ya shafi jiha ne kuma gwamnati tana da alhakin yin abin da ya dace ga jihar."
"Ina sane da cewa ya bijirewa duk wani matsin lamba domin ganin gwamnatin tarayya ta shiga lamarin."

- Muhammadu Sanusi II

Aminu Ado Bayero ya shiga fada

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya dawo birnin Kano bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cire shi daga sarauta.

Taohon Sarkin na Kano ya wuce kai tsaye zuwa ƙaramar fada wacce ke a gidan Sarki da ke Nasarawa a cikin birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel