Wahalar man fetur a Najeriya
'Yan kasuwa sun ce ba za a ga raguwar farashin man fetur nan take a gidan mai ba. Dangote ya rage farashi, amma gidajen mai na da man da suka saya a tsohon farashi.
Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N890, inda kamfanin ya bukaci ‘yan kasuwa su bi sahu. Jama’a na jiran ganin ko ragewar za ta kai ga kowa.
Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta PETROAN ta ce nan gaba kadan za a samu saukin farashin man fetur a Najeriya saboda farfado da matatun Fatakwal da Warri.
Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Bƴhari, Rotimi Amaechi, ya bayyana shirinsa da ya zama shugaban kasan Najeriya.
Yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa an samu saukin kudin shigo da litar man fetur daga ketare. Hakan na nufin za su iya daina sayen mai a matatar Dangote.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an samu masu zuba hannun jari da su zuba hannun jarin Daloli a Najeriya, wanda aka yi fatan zai inganta kasar .
Kamfanin NNPC ya kara farashin man fetur zuwa N990 a Abuja da N965 a Lagos. An bayar da lasisin matatar mai a Delta ga kamfanin MRO Energy Limited.
Matatar Ɗangote ta bayyana cewa ta yi rago sosai a karin farashin man fetur da ta yi a baya-bayan nan, inda ta fadi wuraren da za sane shi a kasa da ₦1,000.
Sakamakon hauhawar farashin gangar ɗanyen mai a kasuwar duniya, farashin tataccen ɗanyen man fetur ya tashi a wuraren ƴan kasuwa bayan ƙarin da Ɗangote ya yi.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari