'100%': Bayan Watanni 22, Matatar Dangote Za Ta Fara Aiki Yadda Aka Tsara
- Kamfanin Dangote ya bayyana cewa matatarsa mai mafi girma a Afirka na iya cimma 100% na karfinta cikin a cikin kwanaki masu zuwa
- Matatar Dangote, wacce ke Legas, ita ce mafi girma a Afirka kuma daya daga cikin manyan matatun mai a duniya dake tace mai a yanzu
- Shugaban matatar, Edwin Devakumar ya tabbatar da cewa an fara sayar da wasu daga cikin kayayyakin da ake tace wa zuwa kasashen waje
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kamfanin Dangote ya bayyana cewa matatarsa, wacce ita ce mafi girma a Afirka, na iya fara cimma tace danyen mai a cikin kwanaki 30.
Shugaban matatar, Edwin Devakumar, ya ce matatar mai mai karfin tace fetur 650,000 da Aliko Dangote ya gina a Legas ta fara sarrafa danyen mai a cikin Janairun bara sannan ta fara sarrafa fetur a watan Satumba.

Asali: Facebook
Reuters ta wallafa cewar Mista Devakumar ya nuna cewa matatar na da burin yin kafada-da-kafada da matatun Turai idan ta fara aiki a matakin 100%.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kamfanin ya tabbatar da cewa ta na fuskantar matsalar samun isasshen danyen mai a cikin gida.
Yadda matatar Dangote ta taimaka wa Najeriya
ThisDay ta ruwaito cewa matatar da kamfanin Dangote ya gina na daya daga cikin mafi girma a duniya kuma ita ce mafi girma a Afirka.
An samar da katafaren matatar da ke Legas ne domin sarrafa ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana, wanda hakan ke zama wani sabon abu a bangaren makamashin Najeriya.
Matatar, wacce aka kashe Dala biliyan 20 wajen ginawa, ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da mai daga kasashen waje tare da cika bukatun cikin gida na man fetur.
Matatar Dangote za ta kara yawan tace mai
Shugaban matatar Dangote, Edwin Devakumar, ya ce a halin yanzu matatar tana aiki da 85% na karfinta, amma ana sa ran cimma 100% a cikin wata guda.

Kara karanta wannan
Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji
A bara, matatar ta koma shigo da danyen mai daga waje bayan kasa samun isasshen mai daga cikin Najeriya, duk da yarjejeniyar da aka kulla da gwamnati na sayen danyen mai da Naira.
Dangote zai shiga kasuwar duniya
Matatar Dangote na kokarin samun sababbin kasuwanni domin sayar da kayayyakin da ta ke sarrafa wa, daga ciki har da man fetur.
A makon da ya gabata ne, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce sun tura jiragen ruwa biyu dauke da man jiragen sama zuwa kamfanin Saudi Aramco a matsayin wani bangare na shirin fadada kasuwa.
Matatar Dangote ta rage farashin fetur
A wani labarin, mun wallafa cewa daga 1 ga watan Fabarairu ne matatar man Dangote ta ce za a fara cin moriyar ragin farashin man fetur da take sayarwa daga N950 zuwa N890 kowace lita.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da jami’in mai kula da sadarwa na kamfanin, Anthony Chiejina,kuma an ce rage farashin yana da alaka da sauyin yanayin kasuwannin makamashi na duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng