Gobara
Gobara ta lalata gidan amarya da wasu gidaje shida a Zamfara. An ce motocin kashe gobara sun samu matsala, lamarin da ya jawo wutar ta babbake dakin amaryar.
Isra'ila ta bayyana kokarin da take na kashe gobarar da ta tashi a bayan shafe sa'o'i 30 ba tare da kammala kashe gobarar ba. An kama wasu mutane kan tashin wutar.
Mummunar gobara ta tashi a kasuwar wayoyi ta Ilorin. An ce wutar lantarki ce ta haddasa gobarar. An dakile wutar cikin lokaci amma rumfuna 10 sun kone.
Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Sani Yahya Jingir ya nuna alhini kan gobarar da ta tashi a kasuwar Taminus da ke Jos inda ya shawarci gwamnati da masu arziki.
An samu tashin wata mummunar gobara wacce ta jawo asarar dukiya a birnin Kano. Gobarar ta lakume shaguna da ajujuwa da dama a unguwar Rijiyar Zaki.
Gobara a kasuwar Gandun Albasa ta kone shaguna hudu a Kano. Asara ta kai miliyoyin naira, amma an dakile bazuwar wutar. An samu ceto a wasu shaguna.
Gobarar kasuwar Zamfara ta kone shaguna 55, inda ta shafi sashen masu sayar da magungunan gargajiya. 'Yan kasuwa sun roƙi gwamnati ta kai masu dauki.
Al'ummar Kano da ke zaune a Kofar Nasarawa sun shiga tashin hankali da gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero' wanda yake matsayin matsugunnin jami'ar Arewa maso Yamma.
Gobara ta babbake sabon ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Sokoto. An tabbatar da babu asarar rai, amma hr yanzu ba a kai ga tantace girman barnar da ta yi ba.
Gobara
Samu kari