Gobara
Wata tankar dakon mai da ta fashe fetur ya fara kwarara ta kama da wuta bayan mutane sun gana kewaye ta, ana fargabar rasa gomman rayuka a jihar Neja.
'Yan kasuwa da dama sun shiga jimami bayan tashin wata gobara a jihar Anambr a. Gobarar wacce ta tashiɓda tsakar ta jawo asarar kayayyakinna miliyoyin naira.
Trump ya soki shugabannin California kan gobarar da ta kashe mutum 24, ya ce ba su iya shawo kan matsalar ba. Gwamna Newsom ya gayyace shi ya ga barnar da kansa.
Gobarar dare ta halaka Jumai Sunday da ɗanta a Kugbo da ke Abuja. An gano gawarsu bayan kashe wutar, kuma 'yan sanda sun fara bincike kan lamarin.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bada tabbacin cewa za ta tallafawa mutanen da iftila'in mummunar gobara ya shafa a kasuwar Karar 'Yan Nika da ke jihar.
Allah ya yi wa diyar sakataren gwamnatin jihar Sakkwato da yayanta uku rasuwa sakamakon wata gobara da ta kama a gidansu, an fara shirye-shiryen jana'iza.
Mazauna jihar Ribas sun fada fargaba a lokacin da wata tukunyar gas ta tarwatse ana tsaka da gyaranta, har ta farfasa wasu shagunan ta fito har bakin titi.
An samu tashin mummunar gobara a wata fitacciyar kasuwa da ke jihar Sokoto. Gobarar wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar ta lalata shaguna masu yawa.
Wani ibtila'in gobara ƴa afkawa caji ofis na ƴan sanda a jihar Legas, lamarin ya fara ne daga wata tanka da ke sauke man dizel a wani otal da ke kusa da ofishin.
Gobara
Samu kari