Gwamnatin tarayyar Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori Ahmed Halilu, dan uwan Aisha Buhari, daga shugabancin kamfanin buga kudi na Najeriya. Ya hada da wasu mutane hudu a kamfanin.
Shugaba Bola Tinubu ya yi babban alkawari yayin da yake martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke na baiwa kananan hukumomi cin gashin kai kan gwamnoni 36.
Rahotanni sun bayyana cewa mai tsaron lafiyar shugaban kasa Bola Tinubu na shirin darewa kujerar Sarkin Ilemona da ke hedikwatar karamar hukumar Oyun a jihar Kwara.
Gwamnatin jihar Adamawa karkashin gwamna Ahmadu Fintiri ta maka gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a kotu bisa zargin zaftare mata kudin wata wata.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori takwas na tarayya. Shugaban kasan ya ba su rantsuwar kama aiki ne a fadarsa da ke Abuja.
Majalisar wakilai ta fito ta yi magana kan batun dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da yarjejeniyar Samoa. Majalisar ta ce sam ba ta yi hakan ba.
Shugaba Bola Tinubu ya kirkiro ma'aikatar raya dabbobi. An sanar da kirkirar ma’aikatar ne a yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da gyara kan harkokin kiwon dabbobi.
Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa za ta hakura ne kawai da shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi.
Gwamnatin Tinubu ta ce babu wani lamunin $150bn ko kuma amincewa da 'yancin ‘yan madigo, 'yan luwadi, 'yan daudu, da masu auren jinsi a cikin yarjejeniyar Samoa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari