Gwamnatin Tarayya za ta Sake Zama da NLC kan Mafi Karancin Albashi

Gwamnatin Tarayya za ta Sake Zama da NLC kan Mafi Karancin Albashi

  • A ranar Talata 21 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya za ta sake zama da kungiyoyin kasar nan kan batun mafi karancin albashi da zummar cimma matsaya
  • A Larabar da ta gabata ne kungiyar kwadago ta NLC ta fice daga taron da kwamitin duba kan mafi karancin ta kira saboda rashin amincewa da matakin da su ka dauka
  • Kwamitin karkashin Bukar Goni ya bawa gwamnati shawarar ta biya mafi karancin albashin N48,000, lamarin da NLC ta zai ba zai yiwu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya za ta sake zama domin ci gaba da tattauna batun mafi karancin albashin da kungiyoyin kwadago ke ta fafutukar a yi wa gyara.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

Kwamitin da gwamnati ta kafa kan sabon mafi karancin albashin ya dauki matakin sake zama ne bayan ‘ya’yan kungiyar NLC ta fice daga tattaunawar da su ka fara a ranar Larabar da ta gabata.

Kungiyar NLC
Kwamitin gwamnatin tarayya za ta sake zama da kungiyar NLC Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya amince da sake yin gyaran fuska a kan mafi karancin albashin N48,000 da su ka fitar tun da fari, kamar yadda aminiya ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ya gayyaci NLC sabon zama

A wata wasika da ya aikewa kungiyoyin kwadagon kasar nan, Bukar Goni ya bukaci shugabannin kungiyoyin su gayyaci ‘ya’yansu domin sake zama a ranar ranar Talata 21 ga watan Mayu.

Su dai kungiyoyin kwadagon sun sun nemi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata, kamar yadda BBC ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Ba ka da lissafi ko kadan": Kungiyar TUC ta ɗaga yatsa ga Tinubu kan karin albashi

Amma kudin da kwamitin ya bijiro da shi ya yi hannun riga da abun da su ka yi fatan za a amince a biya ma’aikatan.

Tuni dai kamfanoni masu zaman kansu su ka amince da bawa ma’aikatansu N54,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Gwamnan Lagos ya musanta karin albashi

A baya mun kawo mu ku labarin yadda gwamnatin Lagos ta musanta cewa ta karawa ma’aikatan jihar albashi zuwa N70, 000 kamar yadda ake yayatawa.

Kwamishinan yada labaran jihar, Gbenga Omotosho ya bayyana cewa an yi wa furucin Gwamna Sanwo Olu mummunar fahimta, amma bai ce an yi karin albashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.