A Karo Na 2, Ƴan Kwadago Sun Yi Fatali da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya

A Karo Na 2, Ƴan Kwadago Sun Yi Fatali da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta sake fuskantar tirjiya daga ƴan kwadago bayan gabatar da sabon mafi ƙarancin albashi a karo na biyu
  • Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya sun sake yin watsi da tayin N54,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a taron yau Talata
  • Ƴan kwadagon sun bayyana cewa ba za su yarda da N100,000 ba duba da halin matsin tattalin arzikin da aka shiga a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A karo na biyu ƴan kwadago a Najeriya sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashin da gwammatin tarayyata gabatar.

An tattaro cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta gabatar da N54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a wurin taro yau Talata.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": ASUU ta sanar da shirin shiga yajin aiki a dukkan jami'o'in Najeriya

Yan kwadago a Najeriya.
Gwammatin tarayya ta ƙara fuskantar tirjiya daga ƴan kwadago kan mafi karancin albashi Hoto: Nigerian Labour Congress
Asali: Getty Images

Kwadago da dambarwar karin albashi

Hakan na nufin gwamnatin ta ƙara yawan mafi ƙarancin albashin daga N48,000 da ta gabatar a karon farko, wanda ƙungiyoyin kwadagon suka ce ba za ta saɓu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ƙarawa zuwa N54,000, manyan ƙungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun sake yin watsi da tayin nan take, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin shugaban kwadago na ƙasa wanda ya samu halartar taron da aka gudanar yau, ya tabbatar da cewa ba za su karɓi sabon tayin gwamnati ba.

Albashin nawa NLC take so daga gwamnati?

A makon jiya kungiyar kwadago ta ce buƙaci gwamnatin tarayya ta ma daina tunanin gabatar da tayin N100,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Bayan haka ƴan kwadagon sun roki ɓangaren gwamnati da su ɗauki batun mafi ƙarancin albashi da muhimmanci domin ba za ta yarda ya wuce watan Mayu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gabatar da sabon mafi karancin albashin da take son biyan ma'aikata

Sun kuma ƙara nanata cewa sun riga sun yanke cewa mafi ƙarancin albashin ba zai yi ƙasa da N615,000 duba da halin ƙunci da wahalhalun tsadar rayuwa, cewar The Nation.

ASUU na shirin shiga yajin aiki

A wani rahoton kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta ce da yiwuwar za ta ayyana shiga yajin aiki kowane lokaci daga yanzu.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ƙeƙashe ƙasa, ta ƙi cika wa ASUU bukatunta na tsawon shekara da shekaru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262