Gwamnatin Tinubu Ta Gabatar da Sabon Mafi Karancin Albashin da Take Son Biyan Ma'aikata

Gwamnatin Tinubu Ta Gabatar da Sabon Mafi Karancin Albashin da Take Son Biyan Ma'aikata

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta gabatar da sabon mafi ƙarancin albashin da take son biyan ma'aikata a Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyoyin ƙwadago sun yi fatali da N48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da gwamnatin ta gabatar
  • Wani majiya a taron da aka gudanar a ranar Talata, 21 ga watan Mayu ya ce gwamnati ta gabatar da N58,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta ƙara abin da za ta biya ma'aikata a matsayin mafi ƙarancin albashi zuwa N54,000.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun haƙiƙance cewa mafi ƙarancin albashi na N30,000 a halin yanzu ba zai iya samar da walwala ga ma’aikatan Najeriya ba.

Kara karanta wannan

A karo na 2, ƴan ƙwadago sun yi fatali da sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta gabatar da sabon mafi karancin albashi
Gwamnatin tarayya ta gabatar da N54,000 matsayin mafi karancin albashi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, wannan ci gaban ya biyo bayan rashin yardar ƙungiyoyin ƙwadago da mafi ƙarancin albashi na N48,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashi: An yi baram-baram da ƴan ƙwadago

A taron da gwamnatin tarayya ta kira a ranar Laraba, 15 ga watan Mayu, domin tattauna batun mafi ƙarancin albashin, ƙungiyoyin ƙwadago sun fice daga taron.

Da yake magana a madadin ƙungiyar ƙwadagon, Joe Ajaero, shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), yayi Allah wadai da shirin gwamnatin tarayya na biyan N48,000.

Ya ce gwamnati ba da gaske take ba wajen tattaunawa da ƴan ƙwadago, inda ya ƙara da cewa gwamnati tana da wa'adin zuwa ƙarshen wata domin ta yanke hukunci.

Nawa ne sabon mafi ƙarancin albashi?

Sai dai jaridar The Punch ta ruwaito a yammacin ranar Talata, 21 ga watan Mayu, cewa "wani majiya mai tushe" a wani taro da ke gudana a Abuja ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar ƙara mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

'Yan Kwadago Sun Ƙara Daukar Zafi, Sun Ba Tinubu Wa'aɗi Ya Janye Ƙarin Kuɗin Wuta

Majiyar ya bayyana cewa:

"A yanzu gwamnatin tarayya ta gabatar da ƙudirin Naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi."

Har yanzu dai ba a bayyana ko za a amince da wannan tayin ba saboda matsayar gwamnatin tarayyar ba ta kai N615,000 da ƙungiyoyin kwadago suke son a biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.

TUC ta caccaki gwamnatin tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta TUC ta yi fatali da tayin gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi.

Ƙungiyar ta TUC ta ce kwata-kwata babu hankali kan gabatar da N48,000 da gwamnatin ta yi a matsayin mafi ƙarancin albashin da za a biya ma'aikata a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel