Shugaba Bola Tinubu Ya Aikawa Jiha Kayan Abinci, Gwamna Ya Karbi Buhuna a Arewa

Shugaba Bola Tinubu Ya Aikawa Jiha Kayan Abinci, Gwamna Ya Karbi Buhuna a Arewa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika tarin kayan abinci ga gwamnatin jihar Zamfara a jiya Litinin, 20 ga watan Mayu
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya tabbatar da karbar kayan abincin tare da bayyana adadinsa da yadda za su raba shi
  • Har ila yau gwamna Dauda ya mika godiya ga shugaban kasa bisa taimakon da jihar ke samu wajen magance matsalolin ta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - A safiyar jiya Litinin ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika tarin kayan abinci ga gwamnatin jihar Zamfara.

Jihar Zamfara
Gwamnati ta kaddamar da raba kayan abinci ga talakawa a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnatin Zamfara ta karbi abinci

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da cewa kayan sun iso jihar kuma za ta fara raba su ga wadanda ya kamata ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya karbi kayan aminci ton 42,000 daga gwamnatin tarayya.

Yaushe za a raba kaya abincin?

Gwamnan jihar ya tabbatar da cewa sun kaddamar da fara raba kayan abincin a jiya Litinin, 20 ga watan Mayun 2024.

Kuma za su cigaba da raba abincin daga jiya har sai ya kare domin rage radadin da al'umma jihar ke ciki.

Su wanene wadanda za a rabawa abincin

Duk da cewa gwamnan jihar bai bayyana dukkan nau'o'in kayan da suka karba daga gwamnatin tarayya ba, amma ya bayyana wadanda za su rabawa.

Ya ce za a raba kayan ne ga yan asalin jihar Zamfara da ke cikin tsananin bukata da kuma wasu makarantu da za a zaba.

Gwamna Lawal ya yiwa Tinubu godiyan abinci

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

A lokacin kaddamar da rabon kayan, gwamna Dauda Lawal ya mika godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu a amdadadin daukacin al'ummar jihar

Gwamnan ya ce shugaban kasa na ba su taimako yadda ya kamata kan magance matsaloli tsaro a jihar.

Ya kuma kara da cewa lallai taimakon da suka samu, cikin har da kayan abincin, zai rage radadin tsananin rayuwa da al'ummar jihar ke ciki.

An rufe raba abinci a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ta rufe kofar raba tallafin kayan abinci ga mazauna jihar Gombe.

Gwamnan da ya bayyana haka a wurin bude kamfanin takin zamani a jihar ya ce duk wanda ya ke son cin abinci ya dauki fatanya ya koma gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel