Babban kotun tarayya
Wata kungiya ta shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan jam'iyyar Labour Party (LP). Kungiyar ta nemi a soke rajistar jam'iyyar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da alkalai 9 na babbar kotun jihar Kano da kuma khadi 4 na kotun ɗaukaka ƙara ta shari'ar musulunci.
Babbar kotu da ke jihar Kano ta dauki mataki kan gwamnatin jihar da majalisa inda ta dakatar da su kan gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi guda uku.
Bayan kammala binciken kwakwaf, Gaskiya ta bayyana kan zargin wawure dala miliyan 6.2 daga bankin CBN da aka cire da saka hannun bogi na Buhari a 2023.
Watanni biyu kacal bayan ɓaɗa shi a matsayin alkalin babbar kotun jihar Nasarawa, Mai shari'a Benjamin Makama, ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah da ake tsare da shi, Bello Bodejo, ya shigar da gwamnati kara a gaban kotu yana neman a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
Babbar kotun tarayya mai zama a birnin Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ba ta da ikon binciken tsohon Gwamna Ganduje.
Yayin da ake ci gaba da shari'ar zaben jihar Bayelsa, jami'yyar APC da dan takararta a zaben jihar sun bukaci a rusa alkalan shari'ar zaben jihar.
Wata mata a kusa da Abuja, Jane Ebi, a ranar Juma’a ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta Monday saboda neman mata da yake yi, ta ce ta gaji.
Babban kotun tarayya
Samu kari