Gaskiya Ta Fito Kan Satar $6.2m a CBN da Sa Hannun Buhari Bayan Gudanar da Bincike

Gaskiya Ta Fito Kan Satar $6.2m a CBN da Sa Hannun Buhari Bayan Gudanar da Bincike

  • Gaskiya ta bayyana kan zargin wawure dala miliyan 6.2 daga bankin CBN da aka cire da saka hannun bogi na Buhari a 2023
  • Masanin binciken kwakwaf, Bamaiyi Haruna ya tabbatar da zargin amfani da saka hannun Muhammadu Buhari wurin kwashe makudan kudaden
  • Wannan na zuwa ne bayan EFCC ta yi zargin yin amfani da saka hannun Buhari da tsohon sakataren gwamnatin tarayya don kwashe kudaden

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Masanin binciken kwakwaf, Bamaiyi Haruna ya tabbatar da zargin yin amfani da saka hannun Buhari wurin kwashe $6.2m daga bankin CBN.

Haruna ya ce tabbas zargin da hukumar EFCC ke yi ya tabbata bayan gudanar da bincike mai zurfi kan takardun saka hannun, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

An bankado asirin wawure $6.2m daga CBN domin ba masu kula da zabe
Ta tabbata sa-hannun Buhari aka kwaikwaya wurin yashe $6.2m a 2023. Hoto: Muhammadu Buhari, Godwin Emefiele.
Asali: Facebook

Wane zargi EFCC ke yi kan Emefiele da Buhari?

Idan ba a manta ba hukumar EFCC ta yi zargin cewa an yi amfani da saka hannun Buhari da tsohon sakataren gwamnatin tarayya domin kwashe kudaden.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin an kwafi sa-hannun Buharin da sakataren gwamnatinsa a watan Faburairun 2023 lokacin da tsogon shugaban ke mulki, Ripples ta tattaro.

Hukumar ta ce tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya hada baki da wani mai suna Odoh Ocheme wanda yanzu haka ya gudu wurin aikata badakalar.

Emefiele da Odoh sun kwaikwayi sa- hannun Buharin wurin yashe $6.2m daga bankin CBN da nufin cewa sakataren gwamnatin ne ya bukaci hakan.

Sakamon binciken da aka yi

Wannan bayani na dauke ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Janairun 2023 kamar yadda rahoton ya tabbatar.

Kara karanta wannan

An garkame fursunoni 300 a gidan yarin Kano ba tare da aikata laifin komai ba, in ji ‘yan sanda

Rahoton ya tabbatar da cewa an yi bincike kan asalin sa-hannun nasu inda aka gano sa-hannun Buhari ko Boss Mustapha ya bambanta da na jikin takardun.

Ya ce a karshe binciken ya tabbatar da cewa sa-hannun bogi ne wanda aka kwaikwaya musamman domin satar kudin a cewar Nairametrics.

An fadi yadda Emefiele ya cire dala miliyan 6.2

Kun ji cewa wani ma’aikacin bankin CBN ya bayyana yadda aka cire dala miliyan 6.2 domin masu kula da zabe.

Ogau Onyeka ya ce an cire kudaden ne daga bankin CBN domin ba masu kula da zaben da aka gudanar a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel