APC Ta Shiga Mugun Hannu Yayin da Ta Nemi Soke Kotun Shari'ar Zaben Gwamnan PDP Kan Wani Dalili

APC Ta Shiga Mugun Hannu Yayin da Ta Nemi Soke Kotun Shari'ar Zaben Gwamnan PDP Kan Wani Dalili

  • Jami'yyar APC da dan takararta a zaben jihar Bayelsa sun bukaci a rusa alkalan shari'ar zaben jihar
  • Timipre Sylva Sylva na zargin nuna wariya yayin shari'ar da suke kalubalantar zaben Gwamna Douye Diri na PDP
  • Hakan ya biyo nasarar da Diri na jam'iyyar PDP ya samu a zaben da aka gudanar a watan Nuwambar 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Alkalin kotun sauraran kararrakin zaben jihar Bayelsa ya dage sauraran karar jihar har sai baba ta gani.

Alkalin kotun da ke birnin Tarayya Abuja ya dauki matakin ne kan korafin da APC da dan takararta, Timipre Sylva suka shigar.

Kara karanta wannan

Kungiya ta yi kira ga Abba ya dawo da tsarin masarauta 1 a Kano, a rushe Rano, Gaya, Bichi da Karaye

APC ta gamu da matsala yayin da bukaci rushe kotun zabe a wata jiha
APC da Sylva na zargin nuna musu wariya a shari'ar da ake yi. Hoto: Douye Diri, Umar Ganduje, Timipre Sylva.
Asali: Facebook

Menene korafin APC Kan shari'ar Bayelsa?

Dalilin dage karar shi ne bai wa shugaban Kotun Daukaka Kara daukar mataki kan zargin nuna wariya da Sylva da APC ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'yyar APC da dan takararta a zaben jihar Bayelsa sun bukaci a rusa alkalan shari'ar zaben jihar, cewar Channels TV.

Suna zargin kotun da rashin ba su damar fadin albarkacin bakinsu kan shari'ar kamar yadda doka ta tanadar.

Har ila yau, sun yi zargin an ba su damar gabatar da shaidu 25 a kullum amma takwas kawai suke samun damar gabatarwa.

Sylva da APC na kalubalantar zaben Diri na PDP

APC da Sylva sun kuma nuna rashin jin dadi kan take musu hakkinsu na 'yan kasa yayin zaman kotun, cewar Premium Times.

Duk da korafin da APC da Sylva ke yi, alkalin kotun ya ce shi bai ga wani dalili ko hujja kan zargin da suke yi ba.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisar PDP a Arewa ya shiga matsala bayan APC ta masa barazana kan wani dalili

Wannan na zuwa ne yayin da Sylva da APC ke zargin almundahana a zaben Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa da aka gudanar.

Diri ya yi nasara a zaben ne da aka gudanar a watan Nuwambar 2023 inda APC ta sha kaye a zaben.

An rantsar da Diri a matsayin gwamna

Kun ji cewa sabon gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya karbi rantsuwa a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Wannan ya biyo bayan nasarar da Diri na jam'iyyar PDP ya yi a zaben da aka gudanar a watan Nuwambar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel