Kotu Ta Dauki Tsattsauran Hukunci Kan Likitan Bogi da Ake Zargin Ya Kashe Mara Lafiya

Kotu Ta Dauki Tsattsauran Hukunci Kan Likitan Bogi da Ake Zargin Ya Kashe Mara Lafiya

  • Wata kotun majistare ta Iyaganku, jihar Oyo ta dauki mummunan mataki kan likitan bogi da ake zargin ya kashe majinyaci
  • Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Olagunju, ya shaidawa kotun cewa likitan, Olaoluwa, ya yi wa majinyacin allurar 'saline' ya mutu
  • Wannan laifin da Olaoluwa ya aikata, ya sabawa sashe na 316, da kuma hukunci a karkashin sashe na 319 da 484 na dauri da kisa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Oyo - Kotun majistare ta Iyaganku, ta tasa keyar wani likitan bogi mai shekaru 45, Adegoke Olaoluwa, bisa zargin ya yi sanadin mutuwar wani majinyacinsa.

Alkaliyar kotun, Misis A T Oyediji, ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Agodi da ke Ibadan, har zuwa lokacin da za ta ji daga bakin ofishin kula da kararrakin jama’a na jihar Oyo (DPP) kan karar.

Kara karanta wannan

Kotu ta haramtawa magidanci magana da matarsa na tsawon kwana da kwanaki

Kotun majistare ta daure likitan boge a Oyo
Kotu ta na iya yanke hukuncin dauri ko kisa akan likitan bisa wannan laifi da ya aikata.
Asali: UGC

Yadda likitan ya aikata laifin - Olagunju

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Olaoluwa, wanda ke da zama a yankin Idi-Aro a Ibadan, yana fuskantar tuhumar kisan kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da fari, jami'i mai shigar da kara, Sufeta Opeyemi Olagunju, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar a ya aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Sufeta Olagunju ya ce Olaoluwa ya yi sanadin mutuwar wani Adekunle Badmus mai shekaru 45 a asibitin Mercy Clinic and Maternity da ke Idi-Aro, Ibadan.

Wanne hukunci za a iya yanke masa?

Ya ce wanda ake tuhumar ya yi wa majinyacin allurar 'saline' ba tare da wani dalili na doka ba.

The Cable ta ruwaito wannan laifin da Olaoluwa ya aikata, ya sabawa sashe na 316 da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 319 da 484 na kundin laifuffuka na jihar Oyo, 2000.

Kara karanta wannan

N11,000/50kg: Hauhawar farashin siminti da matsalolin da yake haifarwa a Najeriya

Sashi na 484 ya tanadi daurin shekaru uku ga wanda ya aikata laifin, yayin da sashe na 319 ya tanadi hukuncin kisa.

An gurfanar da fasto gaban kotu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, an gurfanar da wani fasto a gaban kotun majistare da ke Abuja bisa kamashi da laifin mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba.

Dan sanda mai gabatar da kara ACP James Idachaba ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar, Uche Aigbe, ya dauki bindigar AK-47 ya hau mimbarin coci yana wa'azi da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel