Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu da Mijinta Saboda Dalili 1 Tak

Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu da Mijinta Saboda Dalili 1 Tak

  • Wata matar aure ta roki alkalin kotun gargadiya da ke Jikwoyi, kusa da Abuja da ya taimaka ya raba aurensu da mijinta
  • Misis Jane Ebi ta zargi mijinta Monday da munanan dabi'a da suka hada da neman matan banza, saurin fushi, mugunta, da shaye-shaye
  • Mai shari'a Doocivir Yawe, ya bukaci ma'auratan da su je gida su yi sulhu a tsakaninsu bayan mijin ya karyata zarge-zargen da ake masa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata 'yar kasuwa mai suna Jane Ebi ta maka mijinta, mai suna Monday, gaban wata kotun gargadiya da ke Jikwoyi, kusa da Abuja a ranar Juma'a.

Me yasa matar ke so a raba aurensu da mijinta?

Matar, wacce ta nemi alkali ya kashe aurenta, tana zargin mijin nata da neman matan banza, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

Misis Ebi ta sanar da kotun cewa mai gidan nata yana da saurin fushi da mugunta, sannan kuma yana da mummunar dabi'a ta shaye-shaye.

Matar aure ta nemi a raba aurensu da mijinta
Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu da Mijinta Saboda Dalili 1 Tak Hoto: Thisday
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta ce:

"Mijina yana yawan kwana da kanan yara mata a wajen gidanmu na aure, inda ya kan bar ni da yara cikin hatsari.
"Na yi iya bakin kokarina don ganin ya sauya wannan rayuwar, amma ya ki canjawa. A kan haka ne name neman rabuwa da shi."

Alkali ya ba ma'auratan zabi

Sai dai kuma, mijin ake kara, wanda ya kasance direban mota, ya karyata duk zarge-zargen da matar tasa take yi masa.

Alkalin kotun, Doocivir Yawe, ya shawarci ma'auratan da su je su yi maslaha a tsakaninsu sannan ya dage zaman har zuwa ranar 7 ga watan Maris, domin jin ko sun yi sulhu ko cin gaba da zaman shari'a, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano rijiyoyi 40 da ake satar danyen man Najeriya a kungurmin kauye

Mata ta roki kotu ta kashe aurenta

A wani labari makamancin wannan, wata mata mai suna Oluwatoyin Falade a ranar Laraba ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta Segun saboda yawan neman mata da yake yi.

Oluwatoyin mai shekaru 44 ta ce sun shafe shekaru 11 suna zaman aure kuma Allah ya azurtasu da ‘ya’ya biyu da mijin nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel