"Yadda Emefiele Ya Ba Matarsa Kwangilar Biliyoyin Naira Lokacin Yana Gwamnan CBN"

"Yadda Emefiele Ya Ba Matarsa Kwangilar Biliyoyin Naira Lokacin Yana Gwamnan CBN"

  • Wani shaida da hukumar EFCC ta gabatar gaban kotu, ya bayyana cewa Godwin Emefiele ya ba matarsa kwangilolin biliyoyin Naira
  • Agboro Omowera, ya sanar da kotun cewa tsohon gwamnan CBN ya kuma ba wani kamfani kwangilar sayen motocin Hilux 45
  • Omowera ya ce tun da Emefiele ya hau gwamnan CBN ya ke ba kamfanin matarsa da na ma'aikaciyar bankin kwangilolin makudan kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Agboro Omowera, wani mai bincike daga hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ya ce tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele ya ba kamfanin matarsa kwangilar biliyoyi.

Omowera ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da ya gurfana gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, domin ba da shaida bisa sahalewar hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Emefiele ya cire daloli daga asusu babu amincewar Buhari ba, fadar shugaban kasa

EFCC ta kawo sabuwar hujja kan Emefiele
EFCC ta kawo hujja kan zargin Emefiele ya ba da kwangiloli ba bisa ka'ida ba. Hoto: @GodwinIEmefiele, @officialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar EFCC ta ce ana tuhumar Emefiele da aikata laifuka 20 da suka shafi zamba cikin aminci, hada baki a yi takardun bogi, sayen kadarori ba bisa ka'ida ba da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laifukan da ake zargin Emefiele ya aikata

EFCC ta zargi Emefiele da yin amfani da mukaminsa wajen ba kamfanin April 1616 Investment Limited, mallakin Sa'adatu Yaro, ma'aikaciyar CBN kwangiloli.

Haka kuma hukumar na zargin tsohon gwamnan CBN din ya ba kamfanin Architekon Nigeria Limited, mallakin matarsa kwangilar biliyoyin Naira.

Ana zargin tsohon gwamnan ya yi amfani da kujerarsa wajen azurta matarsa Margaret da dan uwan matarsa wajen ba kamfanin Architekon kwantirakin.

Emefiele bai ba kansa kwangila ba?

Da ya ke ba da bayani a matsayinsa na shaida ta bakwai da EFCC ta gabatar gaban kotun, Omowera ya ce mutane 10 ne suka saka hannu aka bayar da kwangilolin.

Kara karanta wannan

Mai girkin tsohon gwamna ya shiga matsala bayan wawushe kayan miliyoyin Ambode

Ya shaidawa kotun cewa kamfanin Yaro ya samu kwangilar sayo motoci kirar Hilux wadda aka sayo su a kan N854,700,000 zuwa N99,900,000.

Duk da cewa Omowera ya tabbatar da Emefiele bai ba kansa kwangilar komai ba, sai dai ya ce kamfanin matarsa na samun kwangiloli tun bayan zamansa gwamnan CBN.

Meyasa ba a tuhumi sauran mutane 10 ba?

Ko da aka tambaye sa dalilin da ya sa ba a gayyaci sauran mutane 10 da suka aikata laifin tare da Emefiele ba, Premium Times ta ruwaito Omowera ya ce saboda Emefiele ne shugabansu.

"Akwai mutane 10 da suka saka hannu, amma amincewar mutum daya ce kawai ke da muhimmanci. Don haka shi (Emefiele) shi ne shugaba mai iko a kan komai."

A cewar Omowera.

Ya kuma kara bayyana cewa an yi wa kamfanin April 1616 Investment Limited kwanaki kadan bayan da aka ɗauki Yaro aiki a CBN.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya tona asirin badakalar da Emefiele ya yi ba tare da sanin Buhari ba

Emefiele ya cire kudi ba da amincewar Buhari ba

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa fadar shugaban kasa, ta fayyace yadda tsohon gwamnan CBN ya rinka cire kudi a bankin ba tare da amincewar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Ajuri Ngelale, kakakin Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana cewa Godwin Emefiele shi ne ya ci karensa ba babbaka tare da wadaka da kudin Najeriya ba tare da masaniyar Buhari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel