Gwamnan Jihar Arewa Ya Gwangwaje Manoma 2,040 Na Jiharsa, Ya Yi Abin a Yaba

Gwamnan Jihar Arewa Ya Gwangwaje Manoma 2,040 Na Jiharsa, Ya Yi Abin a Yaba

  • Gwamnatin jihar Katsina ta tallafawa manoma 2,040 da kayan noman rani a wani shiri da take yi na bunkasa sana'ar noman rani a jihar
  • Gwamnan jihar, Dikko Radda ya sanar da ba da tallafin a Funtua, karamar hukumar jihar, inda ya ce shirin zai rage radadin talauci da yunwa
  • Jihar ta samar da kayayyakin noma da za ta ba manoman da suka hada da rijiyoyin bututu guda 204 da injinan fanfo mai amfani da hasken rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da shirin bunkasa noman rani kashi na farko ga manoma 2,040.

Wannan shiri dai na daga cikin yunkurinsa na bunkasa noma tare da inganta samar da abinci a fadin kananan hukumomin 34 na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Haramta Sha da Sayar da Barasa a Wasu Kananan Hukumomi 9 a Jiharsa

Dikko radda ya tallafawa manoma a Katsina
Dikko Radda ya gwangwaje manoma 2,040 a Katsina, zai yaki talauci da bunkasa aikin noman rani
Asali: Twitter

Manufar shirin tallafawa manoman rani a Katsina

Yayin kaddamar da shirin a Gwaigwaye da ke gundumar Dikke, karamar hukumar Funtua, gwamnan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na bunkasa harkokin noma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa shirin na da nufin karfafa gwiwar manoma 2,040 a fadin jihar ta hanyar samar da kayayyakin noman rani kyauta, Leadership ta ruwaito.

Gwamna Radda ya kuma ce yuwuwar shirin zai rage radadin talauci, samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa kudaden shiga a jihar.

Kayayyakin aikin noma da jihar ta samar

Radda ya ba da sanarwar horon da za a yi nan gaba tare da tura jami'an tsawaita aikin gona da za su jagoranci manoma don samun amfanin gona mai kyau.

Kwamishinan noma, Farfesa Ahmed Mohammed Bakori, ya ce manoma 2,040 za su samu tallafin iri, taki, da sinadarai na kashe kwari, shafin gwamnatin Katsina a X ya wallafa.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin tarayya ta fara rabawa talakawa N20,000

Bakori ya kara da cewa gwamnatin jihar ta zuba hannun jari wajen samar da kayayyakin noman rani da suka hada da rijiyoyin bututu guda 204 da injinan fanfo mai amfani da hasken rana a wurare daban-daban.

Gwamna Radda ya tabbatar da daukar malamai 7,325 aiki a Katsina

A wani labarin, Gwamnatin jihar Katsina ta mika takardun kama aiki ga wasu sabbin malamai 7,325 da Gwamna Dikko Radda ya dauka aiki.

Gwamnan Radda ya taya malaman murnar samun aikin tare da yi masu nasiha kan yin aiki tukuru, ya kuma sha alwashin ba su horo na musamman kafin fara aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel