Mutane Sun Kai Hari Rumbun Abinci Tare Da Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi A Jihar Bayelsa

Mutane Sun Kai Hari Rumbun Abinci Tare Da Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi A Jihar Bayelsa

  • Matasa sun fasa rumbun abinci a jihar Bayelsa tare da kwasar kayan abinci mai tarin yawa saboda halin kunci
  • Hukumar NEMA a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an kai harin ne a daren jiya Lahadi
  • Duk da rubewar abincin da ke makare a ma'ajiyar abincin bai hana mutane diba ba tare da sauran kayayyaki ba

Jihar Bayelsa - Wasu mazauna garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa sun kai farmaki a rumbun gwamnati.

Mutanen sun kai farmakin ne a daren jiya Lahadi 27 ga watan Agusta, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Mutane sun fusata tare da fasa rumbun abinci da ke makare a jihar Bayelsa
Duba Da Halin Da Mutane Ke Ciki Ya Saka Wasu Mutane Kai Hari Rumbun Abinci A Jihar Bayelsa. Hoto: Postsubman.
Asali: Twitter

Su wa su ka saci kayan abinci a rumbun?

Ba a tabbatar ba ko a cikin kayan da aka satan akwai tallafin Shugaba Bola Tinubu da ya yi alkawari.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma rahotanni sun tabbatar cewa wurin ajiyar kayan abincin na makare da kayan wanda aka ajiye don rabawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a 2022.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa duk da abincin ya dade da rubewa amma bai hana mutane kwasar shi ba.

Meye hukumomi su ka ce kan sata a rumbun?

Yayin tabbatar da lamarin, Hukumar Kula da Agajin Gaggawa (BYSEMA) ta ce lamarin ya faru a daren jiya Lahadi da misalin karfe 7:45.

Hakan na zuwa ne bayan babban daraktan hukumar, Walamam Igrubia da sauran ma'aikatan hukumar sun bar wurin.

Hukumar ta yi Allah wadai da wadannan bata gari da suka yi wannan aika-aika, cewar Vanguard.

Ta kuma nuna bacin ranta ganin yadda wasu 'yan siyasa musamman 'yan adawa ke son siyasantar da lamarin da ya faru a jihar.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Irin wannan lamari ya faru a jihar Adamawa a karshen watan Yuli inda matasa su ka fasa rumbun gwamnati tare da satar kayan abinci na makudan kudade.

'Yan Sanda Sun Cafke Fiye Da 100 Kan Zargin Satar Abinci A Adamawa

A wani labarin, wasu matasa sun fasa rumbin adana abinci na gwamnati da ke jihar Adamawa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

'Yan sandan jihar sun tabbatar da kama mutane fiye da 100 kan zargin dibar kayan abincin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Sulaiman Nguroje shi ya bayyana haka a ranar Litinin 31 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel