Watanni 6 da Hawa Mulki, Gwamnan Jigawa Ya Nemi Alfarma 1 a Wajen Shugaba Tinubu

Watanni 6 da Hawa Mulki, Gwamnan Jigawa Ya Nemi Alfarma 1 a Wajen Shugaba Tinubu

  • Umar Namadi ya tunawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da aikin noman ranin kwari da aka manta da shi a Jigawa
  • Tun Shehu Shagari ya na kan mulki aka fara kwangilar, bayan shekaru 40 har yanzu ba a iya yin ko rabin aikin ba
  • Gwamna Umar Namadi ya ce dubunnan mutane za su samu aikin yi kuma abinci zai wadata idan dai aka yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Jigawa - Mai girma Umar Namadi na Jigawa, ya roki gwamnatin tarayya ta gaggauta kammala aikin noman ranin kwari da ke jiharsa.

Gwamna Umar Namadi ya bukaci a karasa aiki domin a bunkasa noma a jihar Jigawa, Premium Times ta fitar da rahoton nan jiya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tona gaskiyar halin da Buhari Ya damkawa Tinubu tattalin arzikin Najeriya

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu da Gwamnonin Jihohi Hoto: kwarastate.gov.ng
Asali: UGC

Bola Tinubu zai kafa tarihin shekara 40?

Gwamnan ya ce shekaru kusan 40 da su ka wuce aka fara aikin a lokacin mulkin Shehu Shagari, amma har yau ba a iya kammalawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Marigayi Shugaba Shehu Shagari ta kawo tsarin noman ranin ne da nufin inganta noma domin a iya samun isasshen abinci.

Rahoton ya ce gwamnan ya yi wannan bayani wajen kaddamar da tsarin noman alkalama na kasa wanda za ayi a Hadejiya a jihar Jigawa.

Kiran Gwamnan Jigawa zuwa ga Shugaba Tinubu

"Bari in yi amfani da wannan dama domin kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta aikin noman ranin kwarin Hadejiya.
Aikin yana da damar samar da eka 25, 000 na filin noman rani kuma da damar cin ma manufar Tinubu na samun abinci.
Gwamnatin Shehu Shagari ta fara aikin noman ranin kwari a farkon shekarun 1980s, har yanzu bai fi 25% kurum aka yi ba."

Kara karanta wannan

Wike: N15bn ake bukata a karasa gidan mataimakin shugaban kasa da aka fara a 2013

- Umar Namadi

Kokarin Buhari kafin zuwan Bola Tinubu

Namadi ya ce a shekarar 2018 aka farado da aikin, Muhammadu Buhari ya kaddamar da bangaren kusan eka 6, 000 da za a iya noman rani.

Daily Trust ta rahoto gwamnan ya na cewa karin wurin noman da aka samu ya taimaka a lokacin da ake kokarin kara attajirai a Jigawa.

An ci kudin noma a NIRSAL?

Ana da labari Aliyu Abdulhameed wanda ya rike shugabancin NIRSAL ya burma hannun jami’an tsaro kan zargin satar dukiyar gwamnati.

Ana tuhumar tsohon jami’in da satar N5.2bn na noman alkalama wanda aka tsara zai inganta rayuwar manoma 20, 000 a Jigawa da kuma Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng