Zaben Shugaban kasan Najeriya
Wasu yan daban siyasa ne sun kai hari rumfunan zabe a yankin Oshodi da Itire a Legas inda suka tarwatsa masu zabe sannan suka kona akwatin zabe a yau Asabar.
Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa INEC ya ve babu wanda za'a hana jefa kuri'a matukar kafin 2:30 na rana yana kan layi a rumfar zabensa.
Jam'iyyar Accord ta janye daga zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu inda ta ayyana goyon bayanta ga Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya nuna damuwa da rashin jin dadi bisa yadda na'uarar tantance masu zabe na BVAS ta ki tantance shi da matarsa a wurin zabe.
Wani matashi mai suna Akayama ya gamu da ajalinsa bayan yan bindiga sun bindige shi yayin da ya je kada kuri’a a yankin Anyigba, a karamar hukumar Dekina, Kogi.
Akalla mutum 15 yan sanda suka kama kan zargin samunsu da kwamfutocin laftof da manhajojin da za a yi amfani da su wajen yin kutse a sakamakon zabe a Katsina.
Babban Sufetan yan sanda na kasa, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa ana fama da kalubale da dama game da zaben shugaban kasa amma jami'ai sun gama shiri.
Mataimakin shugaban kasa ya isa garinsu da nufin ya kada kuri’a a zaben yau. Farfesan ya canza akwatin zabensa ne daga Legas zuwa garin Ikenne a shekarar 2022.
Jam'iyyu 65 sun ce mutum daya ne a cikin ‘yan takaran 2023 ya cancanta. Za a ji cewa wannan mutum guda kuwa shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari