Hukumar Zabe Zaman Kanta Ta INEC Ta Dage Zabe a Rumfunan Zabe 141

Hukumar Zabe Zaman Kanta Ta INEC Ta Dage Zabe a Rumfunan Zabe 141

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana dage zabe a wasu rumfunar zabe 141 a jihar Omo
  • Wannan ya faru ne sakamakon tsaikon da aka samu a rumfanar na sace na'urorin tantance masu kada kuri'u na BVAS
  • An yi zabe a wasu bangarori daban-daban na Najeriya, ba a samu tsaiko ko tashin hankali ba

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dage zabe a wasu rumfunan zabe 141 a jihar Imo da ke Kudancin Najeriya.

Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar, Mahmud Yakubu a yau Asabar 25 ga watan Faburairu a birnin tarayya Abuja.

Dagewar ta shafi zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a yankunan, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An dage zabe a wasu rumfuna 141 a Najeriya
Mahmud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta INEC | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

An kuma ruwaito cewa, shugaban INEC ya ce za a yi zaben a gobe Lahadi 26 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Sakamako: Tinubu ya lashe zabe a rumfarsa, an fadi kuri'unsa da na Atiku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meye ya faru?

Yakubu na magana ne game da abubuwan da aka lura dasu da kuma suka faru a zaben da aka gudanar a kasar.

Ya kuma bayyana cewa, an samu tsaiko yayin da wasu 'yan daba suka sace na'urorin tantance masu kada kuri'a ta BVAS a wasu yankunan Najeriya.

Hakazalika, ya ce 'yan sanda sun yi nasarar kwato wasu daga cikin na'urorin da 'yan daba suka sace, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

"Ina farin cikin fadin cewa tsarin yana tafiya kuma za a bar 'yan Najeriya su yi zabensu a wuraren da lamarin ya faru."

Zaben 2023 da yadda ake ciki

A yau ne dai 'yan Najeriya suka fito domin zaban shugaban kasan da zai gaji Buhari da kuma 'yan majalisun tarayya 468 a zaben 2023.

Hakazalika, nan da mako biyu ne za a yi zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

Zaben bana shine zabe na bakwai da aka yi a Najeriya tun bayan da aka koma mulkin dimokradiyya a 1999.

A wasu rahotanni, kun ji yadda wasu 'yan daba suka sace na'urorin zabe a jihohin Katsina da Delta.

An kwato wasu daga cikin na'urorin, an kuma maye gurbin was don ci gaba da aikin zabe ba tare da wata matsala ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel