Tinubu Ya Yi Nasara a Rumfar da Ya Kada Kuri’a a Jihar Legas, Atiku Ya Samu Kuri’a 1

Tinubu Ya Yi Nasara a Rumfar da Ya Kada Kuri’a a Jihar Legas, Atiku Ya Samu Kuri’a 1

  • Bola Ahmad Tinubu ya fi kowa yawan kuri'u a mazabar da ya kada kuri'arsa a jihar Legas, inji rahotanni
  • Wanda ya bi masa kuwa, Peter Obi ne, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ta leburori
  • Atiku ya samu kuri'a daya yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya lashe zabe a rumfar da ya kada kuri'a a Legas.

An ruwaito cewa, Tinubu ya dirke abokin hamayyarsa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da sauran 'yan takarar jam'iyyu daban-daban.

The Nation ta ruwaito cewa, Tinubu ya yi zabe ne a Ward 3, rumfa ta 85 a Alausa ta Ikeja a jihar ta Legas da misalin karfe 10:20 na safe.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben Akwatin Datti Baba-Ahmed Ya Fito, Ya Sha Kaye a Hannun Atiku

Yinubu ya ci rumfar zabensa
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Adadin kuri'a da masu kada kuri'u

Adadin wadanda aka tantance a rumfar mutum 43 ne, yayin da aka ce akwai mutum 324 da suka yanki katin zabe a rumfar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon gwamnan na Legas ya samu kuri'u 33 yayin da PDP ta samu kuri'a 1 tak.

Jam'iyyar Labour ta su Peter Obi kuma ta samu 8 yayin da jam'iyyar matasa ta YPP ta samu kuri'a 1 tak.

A yau ne ilahirin 'yan Najeriya suka fito domin zaban shugaban da zai maye gurbin Buhari da kuma sake zaba ko maye gurbin 'yan majalisun tarayya a fadin kasar.

Zaben bana ya zo da sabon salon da ba haka ake zabe ba a Najeriya, 'yan kasar na ci gaba da bayyana jin dadi da samun natsuwa wajen kada kuri'unsu..

Burina Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa, cewar gwamna El-Rufai

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sakamakon Zaben Akwatin Atiku Ya Fito, Ya Lallasa Tinubu da Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Kaduna ya bayyana fatansa na alheri ga dan takarar APC Tinubu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya kada kuri'a, El-Rufai ya ce yana addu'ar Allah ya ba Tinubu nasara a zaben na bana.

Ba wannan ne karon farko da gwamnan ke bayyana goyon bayansa da ga Bola Ahmad Tinubu ba, ya sha fadin hakan a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel