Zaben Najeriya
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Athan Achonu ba su halarci wajen taron sa hannu kan zaman lafiya ba.
‘Dan Majalisan da Kotu ta tsige bayan ya bada ratar kuri’u 60, 000 ya yi magana. ‘Dan majalisar na mazabar Kudanci da Gabashin Jos ya ce akwai rashin adalci a kotu.
Zanga-zanga ta barke a wurare daban-daban na Jos, bayan da kotu ta kwace kujerun 'yan majalisar tarayya karkashin jam'iyyar PDP. Maza ta mata ne suka fito kan titi.
Taron cimma yarjejeniyar zaman lafiya da hukumar INEC ta shirya kan zaɓen gwamnan Imo a birnin Owerri, ya zo ƙarshe cikin rigima a tsakanin jam'iyyu.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin rumfunan zaɓe 40 waɗanda ba za a gudanar da zaɓe ba a zaɓen gwamnan jihar Imo na ranar Asabar.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Honarabul Yusuf Datti na jam'iyyar NNPP kujerar dan Majalisar Tarayyar a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam ta jihar Kano.
Wani Malamin addinin Kirista ya fadi dalilin da ya sa dan takarar jam'iyyar SDP, Ajaka, ba zai ci zaben gwamnan jihar Kogi ba. A cewarsa, Ajaka ba shi da sa'a.
Sakataren yada labaran APC ya zargi Peter Obi da gadarar jin ya dace da mulki. Bayan doke shi a zaben shugaban kasa da kotu, APC ta caccaki 'dan siyasar.
Wata kungiya, New Nigeria Diaspora Movement (CNNDM) ta bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus. Kungiyar ta fadi hakan bayan da kotun koli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Zaben Najeriya
Samu kari