Wasu Abubuwa Biyar Da Zasu Taka Rawar Gani a Zaɓen Gobe

Wasu Abubuwa Biyar Da Zasu Taka Rawar Gani a Zaɓen Gobe

  • A na dab da a fara zaɓe a Najeriya, wata cibiya ta fitar da wasu muhimmin abubuwa da za su taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasa
  • Abubuwan guda biyar da aka lissafo suna da matuƙar muhimmanci ga zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya
  • Ƴan Najeriya da dama na fata da burin samun shugabanni nagari waɗanda za su ciyar da ƙasar gaba

Cibiyar Centre for Democracy and Development (CDD) tayi ƙarin haske kan wasu dalilai guda biyar da za su taka rawa wajen nasarar babban zaɓen Najeriya na 2023.

Cibiyar ta lissafo dalilan guda biyar waɗanda da kira su da It listed the five factors, ‘five I’s” Asali, rashin tsaro, hukumomi, labaran ƙarya, rikice-rikice dake ciki da wajen jam'iyyu.

Zaɓen 2023
Wasu Abubuwa Biyar Da Zasu Taka Rawar Gani a Zaɓen Gobe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Waɗannan dalilan wanda CDD tayi nazari akan su, za su tabbatar an yi zaɓe cikin lumana idan har an warware su yadda ya dace. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

Amma dimokuraɗiyyar ƙasar nan ka iya fuskantat tangal-tangal idan hukumomi suka yi kunnen uwar shegu da waɗanann dalilan. A cewar cibiyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilan sune:

1. Asali

Siyasar Najeriya tun da fari tana kasancewa duk wanda ya hau mulki to ƴan ƙabilar sa ko mabiya addinin sa zai fi baiwa fifiko. Hakan ya sanya ake rububin neman mulki ido rufe a ƙasar.

Domin shawo kan wannan matsalar sai jam'iyyu suka fito da tsarin karɓa-karɓa domin marasa rinjaye a dama da su a fannin mulki.

Sai dai jam'iyyar PDP tayi fatali da wannan tsarin inda ta bayar da dama ga kowa ya nemi takarar shugaban ƙasa. Hakan ya sanya Atiku ya lashe takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Maganar samun wakilci da samun mulki lallai abu ne wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen Najeriya, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Yadda Tururuwar Mutane Sukayi Farin Dango A Kano Domin Tarbar Kwankwaso

2. Matsalar Tsaro

Akwai matsalar tsaro sosai a kusan dukkanin yankunan ƙasar nan. Matsalar tsaro na iya zama abinda zai sanya a fara zaɓe kan lokaci a ƙasar gabaɗaya.

Matsalar tsaro babbar barazana ce ga masu kaɗa ƙuri'a, kayayyakin zaɓe, ma'aikatan zaɓe da rumfunan zaɓe sama da 176,000.

3. Hukumomi

Hukumomi suna da muhimmiyar rawar da za su taka a wajen nasarar wannan zaɓen.

Hukumar zaɓe ta INEC itace take da alhakin gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar. Hukumomin tsaro alhakin samar da tsaro da zama ƴan ba ruwan mu duk ya rataya a kan su a lokacin zaɓe.

Sai dai a bayan an sha kawo ƙorafin waɗannan hukumomin da nuna fifiko akan wasu jam'iyyun, a wasu lokutan.

Ɓangaren shari'a shima yana da rawar da zai taka a zaɓen duba da shine zai kula da ƙararrakin da ka iya biyo baya idan aka kammala zaɓen. Saidai shima a baya an sha zargar sa da nuna fifiko ga wani ɓangaren na siyasa.

Kara karanta wannan

Hasashen Zaɓen 2023: Jerin Jihohin Da Kowanne Daga Cikin Manyan Ƴan Takara 4 Zai Lashe Babu Tantama

4. Matsalar yaɗa labaran ƙarya

Labaran ƙarya na yawo kamar wutar daji a wannan zamanin da muke ciki, inda wasu mutane suka koma amfani da kafafen sada zumunta suna yaɗa labarun ƙarya.

Matsalar yaɗa labarun ƙarya ka iya ƙara ruruta wutar rikici a ƙasar nan.

5. Rikice-rikicen jam'iyyu

Kowacce daga cikin manyan jam'iyyu biyu dake kan gaba wajen takarar shugabancin ƙasar nan na fama da rikice-rikice a cikinta.

APC ta fuskanci matsala daga wajen kiristoci waɗanda ba su ji daɗin ɗaukar musulmi a matsayin mataimaki da Tinubu yayi ba.

PDP ta fuskanci rikicin bayan ta ƙi mutunta tsarin ta na karɓa-karɓa, wanda hakan ya haifar da tawagar G5 waɗanda basa ga maciji da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Waɗannan abubuwa guda biyar da aka lissafo a sama ba ƙaramar taka rawa za suyi ba wajen zaɓen shugaban ƙasa na gobe Asabar a Najeriya.

A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya aike da saƙon ta'aziyyar kan mummunan kisan da aka yiwa wani ɗan takarar sanata.

Kara karanta wannan

Saura Kwana Biyu Zaɓe, Tinubu Yayi Wani Babban Kamu A Abuja

An dai halaka ɗan takarar sanatan na jam'iyyar Labour Party a wani mummunan hari da aka kai masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel