Zaben Najeriya
Za a ji yadda jam’iyyar LP ta dawo da wasu kujerunta da APC da PDP su ka karbe. Alkalai sun yi hukunci cewa karamar Ministar kwadago ba ta yi nasara ba.
Kotun daukaka kara ta rusa zaben sanatan LP da ke wakiltar Abia ta Tsakiya, Darlington Nwokocha, ta bayyana Kanal Austin a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun daukaka kara a jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Daniel Amos a matsayin wanda ya lashe zabe, yayin da tayi watsi da karar APC.
Kotun koli ta yi hukunci kan zaben Gwamna Alex Otti na jihar Abia inda ta tabbatar da nasarar Otti a matsayin gwamnan jihar bayan shan kaye a kotun Kano a baya.
Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya ce ba zai ga laifin alkalan kotun daukaka kara da suka kwace kujerarsa ta sanata ba. Kotu ta kwace kujerarsa ta ba APC.
Gwamnatin jihar Kano ta ce tsohon gwamnan jihar, Ganduje, ya ciwo bashin sama da naira biliyan 500 kafin ya sauka. Bashin ya kawo tsaiko wajen gudanar da ayyuka.
Nyesom Wike ya dauki zafi wajen sulhu da Gwamnan Ribas. Nyesom Wike ya zauna da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai domin dinke barakar PDP a Ribas.
Kotun daukaka kara ta yi hukunci a zaben majalisar Tarayya inda ta tabbatar da nasarar Abdulmumin Jibrin na jam'iyyar NNPP tare da korar karar Said Kiru na APC.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa tutocin jam'iyyar APC ga ƴan takarar gwamnanta a zaɓen gwamna na watan Nuwamba na jihohin Kogi, Bayelsa da Imo.
Zaben Najeriya
Samu kari