Hoto, Bayanai Sun Fito Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Sanannen Dan Majalisar Wakilai Da Dala 498,000 Cikin Jaka

Hoto, Bayanai Sun Fito Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Sanannen Dan Majalisar Wakilai Da Dala 498,000 Cikin Jaka

  • Rundunar yan sandan jihar Rivers ta kama dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Port Harourt na 2, Dakta Chinyere da kudin kasashen waje
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Delta, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da hakan tana mai cewa an kama shi da tsabar kudi $$498,100 a cikin motarsa
  • Iringe-Koko ta kuma ce an same shi da wata takarda da ke dauke da wasu sunayen mutane da ake zargin su za a raba wa kudin, ta kara da cewa ana zurfafa bincike kafin a gurfanar da shi a kotu

Jihar Rivers - An kama dan majalisar tarayya na jihar Rivers, Dakta Chinyere Igwe, dauke da makuden kudaden kasar waje da ba a bayyana adadinsu ba.

An kama Igwe, wanda ke wakiltar mazabar Port Harcourt na 2 a majalisar tarayya, a ranar Juma'a ne da safe a Aba Road a Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Mahaifar Shugaban Kasa da Jihohi 3 da Aka Fi Yawan Wadanda Suka Karbi PVC

Wanda ake zargi
Dan majalisar tarayya na jihar Rivers, Chinyere Igwe da aka kama da kudin kasar waje. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Rivers, Grace Iringe-Koko ta tabbatar wa The Punch lamarin.

Karanta sanarwar da yan sandan suka fitar a kasa:

Yan sandan jihar Rivers sun kana Honarabul Chinyere Igwe kan almundahar kudi

"Yan sanda a jihar Rivers da aka tura hedkwatar hukumar zabe na INEC Aba road a yau 24/2/2023 misalin 0245hrs, yayin binciken ababen hawa a hanya, ta kama wani Honarabul Chinyere Igwe, mamba na majalisar tarayya mai wakiltar Port Harcourt II da tsabar kudi $498,100 cikin jaka a motarsa.
"An kuma gano jerin sunayen wadanda za a raba wa kudin. AIG na zabe, AIG Abutu Yaro fdc ya bata umurnin yin masa tambayoyi da gurfanar da shi a kotu.
"Rundunar tana kira ga dukkan yan takara da jam'iyyun siyasa su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar zabe da sauran dokoki.

Kara karanta wannan

Mu Sheikh Dahiru Bauchi Yake Goyon Baya: APC Ta Saki Bidiyon Shehi Yana Magana

"Ana kira ga al'umma su lura da wadannan lambobin domin kai rahoto don wani da abu da zai yi sanadin aikata laifi ko rushe doka da oda: 08032003514, 08098880134."

Sa hannu

SP. Grace Iringe-Koko

Jami'ar Hulda da Jama'a

Rundunar yan sanda na jihar Rivers

Port Harcourt

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada umurnin rufe iyakokin kasa a wani mataki na shirin yin zaben shugaban kasa da yan majalisa a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun hukumar shige da fice na kasa, Tony Akuneme, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce shugaban hukumar, Isah Jere, ya ce za a rufe iyakokin na kwana guda a ranar zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel