Zullumi A Sansanin Atiku Da Obi Yayin Da Babban Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Bayan Tinubu

Zullumi A Sansanin Atiku Da Obi Yayin Da Babban Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Bayan Tinubu

  • Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya yi watsi da takararsa ya koma bayan Bola Tinubu na APC
  • Kachikwu ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja, ranar Alhamis yana mai cewa ya fuskanci gaskiya ba zai kai labari ba
  • A cewar Dumebi, komawar da Peter Obi ya yi zuwa LP ya sa jam'iyyun adamawa sun rage karfi kuma idan ba haka kai suka yi ba APC za ta cigaba da samun nasara

FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Dumebi Kachikwu ya yi watsi da takararsa ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kachikwu, yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu ya ce ya fahimci gaskiya cewa ba zai iya cin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Tsakanin Atiku, Tinubu da Obi

Kachikwu
Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na ADC ya janye wa Bola Tinubu na APC. Hoto: Dumebi Kachikwu
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke bayyana cewa APC ta fi damar lashe zaben, Kachikwu ya ce abin bakin ciki wadanda matsalar rashin kudi da ake fama da shi a kasar za ta fi shafa sune magoya bayan Peter Obi, na jam'iyyar Labour, LP.

Kalamansa:

"A baya ina tunanin cewa jawabi ta ta karshe za ta zama bayyana dalilin da zai sa ku zabe ni amma a yayin da muke shirin zabe cikin awa 48, ya zama dole in fuskanci gaskiya cewa babu yadda ni da Ahmed za mu yi nasara.
"Don haka, zan yi jawabi na daban kuma shine na Najeriya da za ta yi wa kowa aiki."

Kuri'a da aka jefa wa Peter Obi tamkar ta Bola Tinubu ce

Kachikwu ya cigaba da cewa babban jam'iyyar adawa ta samu tangarda saboda rikicin cikin gida, ciki har da rabuwar kanta da ya bawa dan takarar na APC damar nasara.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Ya Munana, Gwamnan Arewa Ya Shirya Yafe Takararsa Saboda a Doke Atiku

Ya kara da cewa:

"Duk wani kuri'a na Peter Obi na Tinubu ne. PDP da jam'iyyar Labour na bukatar juna. Wannan shine gaskiya.
"A matsayin mu na wadanda suka yarda da demokradiyya na gaskiya, ya zama dole shugabannin PDP da Labour su gano yadda za su yi aiki da sauran kananan jam'iyyu don hadin gwiwa mai karfi kafin su tunkari APC.
"Duk wani yunkurin tunkarar APC ba tare da hadin gwiwan ba zai bawa APC damar kara wasu shekaru hudu.
"Baya ga haka, idan ba dai dukkan arewacin Najeriya sun hada kai cikin awa 24 sun zabi dan takarar PDP bane, alamu na nuna dan takarar APC ne zai yi nasara."

Kwankwaso ya bayyana dalilin da yasa aka kai wa magoya bayansa hari

A wani rahoton kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce an so hana shi shiga Kano ya cigaba da shirin zabe ne shi yasa aka kai wa tawagarsa hari a Kano.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu: Na Ga Obi Yan Sharban Kuka, Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Gabannin Zabe

Tsohon gwamnan na Kano ya ce ya gamsu da yadda ya kammala yakin neman zabensa kuma yana fatan samun nasara a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel