Zaben Najeriya
Daniel Bwala, jigon PDP ya ce dole sai jam'iyyun adawa sun hada kai za su iya kwace mulki a hannun Shugaba Tinubu, akasin hakan zai sa ya yi tazarce a 2027.
Wani farfesa a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Nasarawa, Jideofor Adibe, ya ce zaben 2023 kaɗai ya isa a ce shugaban hukumar INEC na ƙasa ya yi murabus.
A cewar Gwamna Adeleke, tun a shekarun 1980 ya so zama mawaki, amma mahaifinsa ya ki amincewa inda ya tura shi makaranta har zuwa Amurka, har ya zama dan siyasa.
Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ta kama dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar, Hon. Ladi Adebutu kan wasu zarge-zarge da suka hada da siyan kuri'u a zabe.
Ana shirin rantsar da Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu matsayin sabon gwamna kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Akwai ‘yan majalisan da su ka rasu tun a shekarar nan ta 2023. Daga baya hukumar INEC za ta shirya sabon zabe domin maye guraben wadannan ‘yan majalisar.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta saka ranar 3 ga watan Faburairun 2024 don sake zabe saboda cike gurbin kujerun da suke babu kowa a fadin kasar.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Abdullahi Ganduje na cikin waɗanda aƙe ganin sun samu nasara mafi girma a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2023.
Shugaban cocin Glorious Mount of Possibility, Fasto David Kingleo Elijah, ya yi hasashen lokacin da kasar nan za ta rabe. Faston ya ce hakan zai faru kafin 2027.
Zaben Najeriya
Samu kari