Zaben 2023: Abin Da Yasa INEC Bata Tura Sakamakon Zabe Yanar Gizo Kai Tsaye Ba, Jigon APC

Zaben 2023: Abin Da Yasa INEC Bata Tura Sakamakon Zabe Yanar Gizo Kai Tsaye Ba, Jigon APC

  • Wani jigon APC Ekene Enefe ya bayyana dalilin da ya hana hukumar zabe mai zaman kanta watsa sakamakon zabe ta yanar gizo
  • Enefe ya bayyana cewa jam'iyyu da suka tabbatar sun fadi zabe ne suka yi hayar masu kutse don sauya sakamakon zabe
  • Enefe ya ce a iya sanin sa wannan dalilin ne ya hana hukumar zabe watsa sakamakon saboda yadda aka dinga kutse ga shafinta na yanar gizo

Wani jigon jam'iyyar APC, Ekene Enefe, ya bayyana cewa wasu jam'iyyu sun gayyaci madatsan yanar gizo daga Rasha da Isra'ila don chanja alkaluman sakamakon zaben 2023, rahoton The Punch.

Enefe, wanda daya ne daga cikin mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya bayyana haka a wata hira ta kai tsaye da gidan talabijin na Arise TV ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: A Yayin Da PDP Da LP Suka Garzaya Kotu, SDP Ta Ce Ta Yarda Da Nasarar Tinubu

Naurar BVAS
Zaben 2023: Abin Da Yasa INEC Bata Tura Sakamakon Zabe Yanar Gizo Kai Tsaye Ba, Jigon APC. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyu, wanda suka yi rashin nasara a kujerar shugaban kasa, sun yi shawarar yadda za su canja sakamakon zabe ta yanar gizo, yana mai cewa dama sun san sun fadi zabe.

An dako hayar masu kutse daga Isra'ila da Rasha su lalata zabe, Jigon APC

Ya ce:

''Ko wacce jam'iyya na da inda take ganin me yake faruwa, sun san sakamakon. Sun san faduwa za su yi kuma suna son shirya wani abu; kuma abin da suke son yi ya danganci watsa sakamakon zaben ta yanar gizo.
''Amma mutane ba su san sau nawa aka yi kokarin kutse a shafin hukumar zabe ba. Kuma jam'iyyu ne da suka gayyoto madatsa daga Rasha da Isra'ila (ina baku bayanan ba ya kamata in fada muku) don yin kutse a shafin yanar gizon hukumar zabe don watsa sakamakon karya su kuma tayar da hargitsi.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

''Babu wanda yayi nasara a cikin su shiyasa wannan zabe, a iya sani na, ba a watsa sakamakon zaben a shafin yanar gizon hukumar zabe ba''.

Ban fita daga jam'iyyar PDP ba, in ji Ayodele Fayose

Jigon jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya karyata rahoton cewa ya fita daga jam'iyyar PDP.

Fayose ya yi karin haske yana mai cewa yana nan daram a PDP amma ya dan koma gefe guda ne don ya samu damar furta wasu maganganu a matsayinsa na dan kasa mai kishi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel