Ku Karbi Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Sultan Ga Yan Najeriya

Ku Karbi Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Sultan Ga Yan Najeriya

  • Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya magantu a kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2023
  • Sarkin Musulmi ya bukaci al'ummar Najeriya da su karbi sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu hannu bibbiyu
  • Ya bayyana cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so a kuma lokacin da ya so kuma babu wanda ya isa ya chanja ko ya kalubalance shi

Mai martaba sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al'ummar Najeriya da su karbi sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sultan wanda ya kasance shugaban kungiyar harkokin addinin Musulunci na kasa ya bayyana cewa Allah ne mai bayar da mulki ga wanda ya so, rahoton The Nation.

Bola Tinubu, zababben shugaban kasar Najeriya a tsaye
Ku Karbi Sakamakon Zaben Shugaban Kasa, Sultan Ga Yan Najeriya Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta nakalto Sultan yana cewa:

Kara karanta wannan

Shugaban Afenifere Ya Aika Gagarumin Sako Ga Tinubu, Ya Roki Atiku, Obi Da Sauran Yan Siyasa

"Shugabanci daga Allah madaukakin sarki ne kuma yana bayar da shi ga wanda yua so a lokacin da ya so sannan babu wanda zai iya kalubalantarsa ko chanja abun da Ya Yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi yayin bikin sarauta da gabatar da sandar iko ga sabon sarkin Dutse na jihar Jigawa, Alhaji Hameem Nuhu Sanusi, Sultan ya bukaci wadanda suka taru a wajen cewa:
"Dan Allah ku goya ma shugabanninku baya, kada ku yi jayayya da su ko bijire masu. Ba za ku iya ja da ikon Allah ba, ku karbe su hannu bibbiyu domin Allah madaukakin sarki wanda ke bayar da mulki ga wanda ya so ne ya nada su."

Amma ya kuma bukaci shugabannin da su yi adalci ga mabiyansu yayin da ya bukaci yan siyasa da su karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

"Kada ku karfafa wani abu da ka iya tarwatsa zaman lafiya," inji shi.

Da yake nasa jawabin, sabon sarkin ya yi alkawarin ci gaba da kyawawan aikin mahaifinsa kuma magabacinsa.

Ku bar Tinubu ya sarara ya yi aiki, Afenifere ga yan siyasa

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar Afenifere ta yi kira ga daukacin yan siyasa da suka fusata da sakamakon zaben shugaban kasa da su guji jefa kasar cikin rikici.

Pa fasoranti, shugaban kungiyar ya bukaci Bola Tinubu da ya tafi da kowa a gwamnatinsa sannan ya hada kan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel