Sanatan NNPP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi

Sanatan NNPP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi

  • Sanatan jihar Bauchi ya sauya sheƙa daga jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) bayan yasha kaye a zaɓe
  • Tuni sanatan ya tattara ƴan komatsansa ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar
  • Sanatan ya koma bayan gwamnan jihar Bauchi inda ya buƙaci duk magoya bayan sa da su yi masa ruwan ƙuri'u a zaɓe mai zuwa

Jihar Bauchi- Ƙasa da sati ɗaya bayan ya sha kashi a zaɓen sanata, sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar New Nigerian People Party (NNPP), Lawal Yahaya Gumau, ya fice daga jam'iyyar.

Sanatan ya tattara ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen sa da ɗaruruwan magoya bayan sa, sun koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar. Rahoton Tribune.

Bauchi
Sanatan NNPP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Bauchi Hoto: Tribune
Asali: UGC

Komawar sa jam'iyyar PDP, ya ƙarawa neman tazarcen da gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed, yake yi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Goyon Bayan Tinubu: Ɗan Takarar Gwamnan Labour Party Na Ruwa, Jam'iyyar Na Shirin Juya Masa Baya

Sanata Lawal Yahaya Gumau ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar ne lokacin da ya jagoranci ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen sa da magoya bayan sa zuwa gidan gwamnatin jihar Bauchi a ranar Juma'a. Rahoton Vanguard

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen da gwamnan yake nema sannan ya umurci duk wasu magoga bayan sa Bauchi ta Kudu da su tabbatar sun kaɗa ƙuri'un su ga gwamnan da sauran ƴan takarar majalisar dokokin jihar na jam'iyyar PDP.

Sanatan yace gwamnan yayi aiki fiye da tsammanin mutanen jihar, saboda haka yana da kyau mutanen jihar su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ganin ya sake zarcewa akan kujerar sa domin cigaba da ƙwararu ayyukan alherin da yake yi.

"Halin gwamnan shine abu mafi muhimmanci da ya janyo ra'ayi na zuwa jam'iyyar. Ƙauran Bauchi mai gida na ne, shugaba na ne kuma malamina ne wanda nake bin sahunsa domin nayi nasara a siyasa." A cewar sa

Kara karanta wannan

Atiku Yayi Magana Kan Peter Obi, Ya Bayyana Babban Naƙasun Da Ya Yiwa PDP

“Na dawo bayan gwamnan ne yanzu saboda ina son mutane na da su kwashi romon dimokuradiyya, sannan bayan nayi bincike mai zurfi, na gano cewa Kauran Bauchi shine yafi cancanta.
"Sannan ayyukan da yayi shine babban dalilin da ya sanya muka dawo wajen sa."

Jam'iyyar Labour Party Ta Caccaki Ɗan Takarar Gwamnan Ta Na Adamawa

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar Labour Party (LP) ta yiwa ɗan takarar gwamnan ta na jihar Adamawa tatas.

Takarar gwamnan da yake yi na fuskantar barazana a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel