“Ku Bar Tinubu Ya Zauna Ya Yi Aiki”: Pa Fasoranti Ya Roki Obi, Atiku Da Sauransu

“Ku Bar Tinubu Ya Zauna Ya Yi Aiki”: Pa Fasoranti Ya Roki Obi, Atiku Da Sauransu

  • An shawarci Bola Tinubu da ya tafi da kowa a gwamnatinsa ba tare da la'akari da banbancin siyasarsu ba don gina hadaddiyar Najeriya
  • Pa Reuben Fasoranti ne ya bayar da wannan sahwarar a sakon taya murna da ya aikewa zababben shugaban kasa
  • Shugaban Afenifere ya kuma bukaci sauran fusatattun yan siyasa da kada su dauki matakin da ka iya tayar da kasar

Shugaban kungiyar dattawan Yarbawa na Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, ya aike sako zuwa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ya shawarci Tinubu da ya zamo mai adalci ga kowa sannan ya guji yin kuskuren da magabatansa suka yi a mulki, PM News ta rahoto.

Tinubu tare da shugabannin kungiyar yarbawa
“Ku Bar Tinubu Ya Zauna Ya Yi Aiki”: Pa Fasoranti Ya Roki Obi, Atiku Da Sauransu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Fasoranti ya ce ya yi matukar mamaki yadda izinin Allah ya baiwa tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi nasarar karade gaba daya jihohin kasar lokacin kamfen din shugaban kasa, sabanin abun da wasu suka so.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

Sakonsa na taya murna na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yanzu kana da damar. Yanzu ne lokaci da za ka tabbatar da nayi gaskiya. Ina rokon Allah ya kasance tare da kai. Wajen aiwatar da haka,ka guji kuskuren wasu da suka gabace ka. Ka hada kan kasar, ka kalla sannan ka kula da kasar a matsayin daya. ka zamo dan tarayya."

Ku bar Tinubu ya zauna ya yi aiki, Fasoranti ga yan siyasa

Fasoranti ya roki sauran yan takarar shugaban kasar da suka sha kaye a zaben da kada su dauki matakin da ka iya haddasa rikici a kasar.

Ya shawarce su da su dauki mataki na doka idan basu gamsu da sakamakon zaben da ba sannan Tinubu da dukkanin wadanda abun ya shafa su zauna su gaggauta sake gina Najeriya da magance matsalolin da kasar ke fuskanta, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: A Yayin Da PDP Da LP Suka Garzaya Kotu, SDP Ta Ce Ta Yarda Da Nasarar Tinubu

Sakon Afenifere:

"A yanzu ina rokon daukacin yan Najeriya da al'ummar kasa da kasa, wadanda suka fusata, kada ku yi abun da zai kunna wuta a Najeriya."

Mu muka lashe zaben shugaban kasa - Datti Baba-Ahmed

A wani labarin, mun kawo a baya cewa abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour Party, Yusuf Datti Bab-Ahmed ya ce sune suka ci zabe don haka za su kwato hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel