Hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta yi bayanin irin cigaban da ake samu a kokarin da ta ke yi na cafke barayi. Tsofaffin gwamnoni da ministoci da kuma tsohon Akanta Janar ake bincike.
Gwamnati ta fara maganar kafa kotun da za rika garkame manya da aka kawo shawarar a kafa kotun da za su rika sauraron shari’ar satar dukiyar jama'a.
Bola Tinubu zai dauko alkali a matsayin Shugaban ICPC, ko a wajen nada Sufetan ‘Yan Sanda na kasa da gwamnan CBN, ya dauko mutanensa ne a lokacin ya na Gwamna
Wanta Baturiya ƴar ƙasar Jamus ta bayyana yadda wani matashi ɗan Najeriya mai yin Yahoo Yahoo ya damfare ta maƙudan kuɗaɗe har N122m da sunan soyayya.
Za a maida Sakatare ya zama sabon Shugaban Hukumar EFCC. Kwanan nan aka gano take-taken Tinubu wajen nadin sabon Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da barayi.
Emmanuel Ibe Kachikwu zai shiga shari’ar Diezani Alison-Madueke a kotun Westminster. Lambar tsohon Ministan ya bayyana bisa zargin karbar rashawa.
Ana shari’a tsakanin Diezani Alison-Madueke da gwamnatin Birtaniya a wani kotu da ke Westminster. Tun da tsohuwar ministar ta bar gwamnati ake wasan kura da ita.
George Turnah wanda ya na da kusanci da Goodluck Jonathan, ya taba zama hadimi na musamman a NDDC zai tafi gidan gyaran hali a sakamakon samun shi da laifi.
Ma'aikata sun gigice da Bola Tinubu ya fara binciken ‘barnar’ da aka yi a bankin CBN. Sannan Gwamnatin tarayya za ta yi bincike a Hukumar NIRSAL inda aka rika sata.
Hukumar EFCC
Samu kari