Hukumar EFCC Ta Karbo Kudin Sata, Ana Binciken Tsofaffin Gwamnoni da Ministoci

Hukumar EFCC Ta Karbo Kudin Sata, Ana Binciken Tsofaffin Gwamnoni da Ministoci

  • Hukumar EFCC ta yi bayanin irin cigaban da ake samu a kokarin da ta ke yi wajen gano dukiyoyin da aka karkatar a gwamnati
  • Dele Oyewale ya nuna N27bn da $19m da aka sace sun dawo cikin asusun gwamnati, har yanzu ana ta gano kudin sata
  • Tsofaffin gwamnoni da ministoci da tsohon Akanta Janar su na cikin wadanda aka samu korafi, ake ta bincike a game da su

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta shaida cewa ta na binciken wasu manya a kasar nan.

Vanguard ta ce a ranar Laraba, hukumar ta shaida cewa ta samu korafi a kan wasu tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci, ana bincike a kai.

Wadanda ake bincike sun hada da jamo’an gwamnatin tarayya kamar yadda mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya fadawa ‘yan jarida.

Kara karanta wannan

Mu 100 Mu Ka Auka Makaranta, Aka Yi Awon Gaba da Yara a 2021 – ‘Dan Bindiga

EFCC.
Manyan jami'an Hukumar EFCC Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

EFCC ta gano N27, 184, 357, 524 da $19, 084, 419

Mista Dele Oyewale ya ce sun iya karbe N27bn da $19m daga wasu bincike uku da ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin hukumar ya na ta samun cigaba kamar yadda doka ta ba mu iko. Mun karbi korafi a kan wasu ma’aikatan gwamnati da-dama

Wasu daga cikinsu tsofaffin gwamnoni, wasu tsofaffin ministoci da jami’an gwamnati. Ina iya fada maku ana bincike a kansu.

Bayanan binciken na mu zai fito fili ba da dadewa ba. Sannan, ana bincike a kan satar da aka tafka a ma’aikatar wuta da sayen kayan gona."

AGF, NDDC da kudin aikin Mambila

A binciken da hukumar ta EFCC ta ke yi ne aka gano yadda aka karkatar da kudin aikin wutan Mambila da Zungeru ga ‘yan canji na BDC.

Daga kudin ne The Guardian ta ce an saye gidaje a garuruwan Abuja, Legas da Kuros Riba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Sabon Nadin Mukami Mai Muhimmanci a Hukumar FCTA

Baya ga N27, 184, 357, 524 da $19, 084, 419 da su ka dawo hannun hukumar, ta ce an samu wasu kudin da ake zargin tsohon AGF ya wawura.

Rahoton ya ce daga cikin N109bn da ake zargin tsohon Akanta ya sace, wani ya maido N12bn sannan an gano kudin da su ka yi kafa a NDDC.

Aminu Maida zai rike NCC

Kun ji labari dazu cewa sabon shugaban Hukumar NCC, Dr. Aminu Maida ya na shaidar PhD, PGD da digirgi na MEngr duk daga kasar waje.

Mahaifin Aminu Maida shi ne Marigayi Wada Maida, amini wajen Muhammadu Buhari. Dattijon ya rasu ya na shekara 70 a duniya a 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel