Daga Ribadu Zuwa Olukoyede: Takaitaccen Tarihin Shugabannin EFCC, Jihohi Da Kuma Yankunansu

Daga Ribadu Zuwa Olukoyede: Takaitaccen Tarihin Shugabannin EFCC, Jihohi Da Kuma Yankunansu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.

Hakan ya biyo bayan murabus din da dakattacen shugaban hukumar, AbdulRasheed Bawa, ya yi daga kan kujerarsa.

EFCC ita ce hukumar gwamnati da aka baiwa aikin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Tsoffin shugabannin EFCC
Bawa Da Sauran Jerin Tsoffin Shugabannin EFCC, Jihohi Da Kuma Yankunansu Hoto: Nuhu Ribadu, EFCC
Asali: Facebook

Tun farko dai Shugaban kasa Tinubu ya bayyana cewa ya yanke shawarar dakatar da Bawa ne domin bayar da damar yin bincike kan ayyukansa yayin da yake ofis biyo bayan manyan zarge-zarge da ake masa na cin mutuncin kujerar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Bayan dakatar da shi, an umurci Bawa da ya gaggauta mika lamuran ofishinsa ga daraktan ayyuka na hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shin Bawa Ya Yi Murabus Bayan Tinubu Ya Dakatar Da Shi a Matsayin Shugaban EFCC?

A cikin haka ne Legit.ng tattaro jerin sunayen dukkanin shugabannin EFCC na baya da na yanzu.

1. Ola Olukoyede (Sabon shugaban EFCC mai ci)

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC, inda ya maye gurbin Abdulrasheed Bawa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya sanar da nadin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.

Olukoyede gogaggen lauya ne wanda ke da shekaru sama da shekara 22 na kwarewa a fannin.

Ya na da kwarewa sosai a harkokin hukumar EFCC, inda a baya ya taba rike mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban hukumar (2016-2018). Ya kuma rike kujerar sakataren hukumar tsakanin 2018 zuwa 2023.

Olukoyede ya fito daga jihar Ekiti, a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, shi ne mutum na farko da ya fito daga Kudancin Najeriya da zai taba rike shugabancin hukumar tun bayan kafa ta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar EFCC Wanda Ya Maye Gurbin Bawa

2. AbdulRasheed Bawa

An dauki tsohon shugaban hukumar Bawa aiki cikin EFCC a 2004 a matsayin jami'in COC1 kuma ya samu horo a kwalejin rundunar yan sanda da ke Ikeja, Lagas.

Ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren ayyuka a hukumar reshen Lagas. An fara nada Bawa a matsayin jagoran tawaga sannan daga bisani ya zama shugaban sashin damfarar kudade, reshen Lagas a watan Mayun 2008.

Nadin na da matukar muhimmanci yayin da ya zama dan sanda na farko da aka nada a matsayin jagoran tawaga a tarihin hukumar.

Bayan nan Bawa ya rike manyan mukamai, ciki harda shugaban hukumar reshen Ibadan, Port Harcourt sannan daga bisa Lagas.

Bawa ya fito daga Jega, jihar Kebbi a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

3. Mohammed Umar Abba

Mohammed Umar Abba ya kasance jami'in dan sanda wanda ya yi aiki a sashin binciken CTGI na EFCC a hedkwata Abuja.

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

An nada shi daraktan ayyuka na hukumar a 2017 mukamin da ya ci gaba da rikewa har zuwa 2020 lokacin da ya karbi rikon shugabancin hukumar daga hannun Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC.

Ya fito daga yankin Tudun Wada da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya.

4. Ibrahim Magu

Magu ya kasance jami'in dan sanda wanda ya yi aiki a matsayin mukaddashin shugaban EFCC daga ranar 9 ga watan Nuwamban 2015 har zuwa lokacin da aka dakatar da shi a ranar 7 ga watan Yulin 2020. An maye gurbinsa da Mohammed Umar a matsayin mukaddshin shugaban EFCC.

An nada Magu a matsayin shugaban EFCC ne bayan Ibrahim Lamorde, wanda ya yi shugabanci sau biyu sannan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shi.

Daga Lamorde har Magu sun yi aiki a lokacin Nuhu Ribadu kuma suna daga cikin mutanen da suka kawo nasara a zamanin Ribadu.

Kara karanta wannan

Sanatoci Na Shirin Karawa Shugaban Kasa Tinubu Karfi a Sabon Yunkuri a Majalisa

Magu dan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ne.

5. Ibrahim Lamorde

Haifaffen dan jihar Adamawa, Ibrahim Lamurde ya kasance jami'in dan sandan Najeriya wanda aka nada a matsayin mukaddashin shugaban EFCC a ranar 23 ga watan Nuwamban 2011 bayan shugaban kasar wancan lokacin, Goodluck Jonathan ya tsige Farida Waziri.

Majalisar dattawa ta tabbatar da Lamorde wanda ya kasance mataimakin sufeto janar na yan sanda a matsayin shugaban hukumar a ranar 15 ga watan Fabrairun 2012.

6. Misis Farida Waziri

Waziri ta kasance kwararriyar jami'ar doka kuma tsohuwar shugabar hukumar EFCC. Ita ta gaji Nuhu Ribadu a wannan kujerar.

Ita ta yi sanadiyar gurfanar da shugaban kasar Najeriya mai ci, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose a kotu kan zargin hamdame kudi, amma ta raba gari da atoni janar na tarayya a wancan lokacin saboda tsaiko wajen yankewa wadanda ake tuhuma hukunci.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Nada Shugaban ICPC, Ana Duba Yiwuwar Dauko Bakano ‘Dan Shekara 71

An haifi Waziri kuma ta taso a Gboko, jihar Benue da ke arewa ta tsakiya.

7. Mallam Nuhu Ribadu (Shugaban EFCC na farko)

Sunan Nuhu Ribadu ya shahara a Najeriya da waje a lokacin da yake shugaban EFCC. Kwararren lauya, Ribadu ya kasance shugaban hukumar EFCC na farko.

Ya shiga harkar siyasa sannan ya yi takarar kujerar gwamnan jiharsa ta Adamawa amma bai yi nasara ba, haka kuma ya nemi shugabancin Najeriya. Jihar Adamawa na a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugabancin EFCC a yanki

Arewa maso gabas - 3

Arewa maso yamma - 2

Arewa ta tsakiya- 1

Kudu maso yamma - 1

Sauran yankuna - 0

EFCC ta aika sammaci ga tsohon ministan Buhari, Hadi Sirika

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, don amsa tambayoyi.

EFCC ta tsitsiye jami'an kamfanin jirgin saman Najeriya kan aikin kaddamar da jirgin da tsohon ministan ya yi a kuraren lokaci a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel