Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

  • An kawo shawarar a kafa kotun da za su rika sauraron shari’ar da su ka shafi satar dukiyar al’umma da rashin gaskiya
  • Irin wannan kotu na musamman za ta yi kokarin yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa a fadin Duniya
  • Lateef Fagbemi (SAN) ya yi maraba da wannan shawara da aka gayyace shi wani taro da kungiyar HEDA ta shirya a Abuja

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta na tunanin kafa kotu na musamman da za ta saurari shari’ar rashin gaskiya a Najeriya.

Punch ta kawo rahoto a ranar Talata cewa wannan yunkuri zai taimaka wajen maganin masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi bayanin nan a jawabi wajen wani taro jiya.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu Ya Jawowa Mahaifinsa Suka Saboda Yawo a Jirgin Shugaban Kasa

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu zai yaki barayi Hoto: @Nosasemota
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu a taron HEDA

Mataimakin darektan gurfanar da jama’a na ma’aikatar shari’a na tarayya, Yusuf Abdullahi Abdulkadir ya wakilci Lateef Fagbemi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Ministan ya na cikin wadanda su ka tofa albarkaci bakinsu a taron da kungiyar HEDA ta shirya kan yaki da rashin gaskiya.

Ministan ya ke cewa rashin gaskiya da satar da ake tafkawa ya addabi Najeriya, saboda haka ya ce kafa kotun IACC zai taimaka.

"Irin wannan kotu za su bada dama wajen shawo kan shari’o’in rashin gaskiya da su ka shafi mutane da kadarori a kasashen ketare.
Zai iya zama karin hanya wajen karfafa yunkurin yaki da rashin gaskiya da sata a kasa.
Barnar da rashin gaskiya ta yi wa cigaba da wadatar Najeriya ba za su misaltu ba."

- Lateef Fagbemi (SAN)

"Ana ba barayi mukamai" - HEDA

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

Da ya tashi na shi jawabin, Vanguard ta rahoto shugaban HEDA, Olanrewaju Suraj, ya na kokawa a kan barayin gwamnati a kasar.

Mista Olanrewaju Suraj ya ce ana ganin yadda marasa gaskiya su ke samun kujerun gwamnoni, ministoci da sauran mukamai.

Majalisa za ta kara karfin Tinubu

Akwai yiwuwar shirin N-Power, GEEP, CCT, NHGSFP za su bar karkashin Ministar bada jin-kai ta kasa kamar yadda rahoto ya zo mana.

Da farko Yemi Osinbajo ya fara kula da NSIP a lokacin ya na mulki, bayan kirkiro ma’aikatar jin-kai, sai tsare-tsaren su ka bar Aso Rock.

Asali: Legit.ng

Online view pixel