Hukumar EFCC
Yayin da shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta zakulo inda ya ke a kasar Kenya inda ta ce za ta dawo da shi Najeriya.
Bobrisky dai dan daudu ne da ya shahara da ikirarin cewa shi mace ce har ma yana cewa yana daf da haihuwa. Amma yau ya tabbatar da cewa shi namiji ne
Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta yanke wa Bobrisky hukuncin ɗaurin watanni 6 ba tare da zabin taraya ba yau Jumu'a, 12 ga watan Afrilu.
Mai shari’a Rahman Oshodi na kotun laifuffuka da ke Legas, ya bayar da belin Godwin Emefiele a kan Naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Masu amfani da kafafen sada zumuta sun hango gemu ya fara tsayawa dan daudu Bobrisky bayan shafe kwanaki a tsare a ofishin EFCC. Ana ta sharhi a soshiyal midiya
Hukumar EFCC ta ce har yanzu tana kan gudanar da bincike game da zargin karkatar da kudi da ake yi wa tsohuwar ministar jin kai Betta Edu da kuma Halima Shehu.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ya unurci a tsare babban jami'in kamfanin Binance a gidan gyaran hali na Kuje.
Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Emefiele tare da Henry Isioma Omoile a gaban kotun mai shari’a Rahman Oshodi kan sabbin tuhume-tuhume 26.
Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) sun cafke wani babban fasto a jihar Kwara kan zargin yin damfarar N3.9m.
Hukumar EFCC
Samu kari