EFCC: An Gano N30bn Bayan Dakatar da Betta Edu da Tsare Sadiyar Umar Farouk

EFCC: An Gano N30bn Bayan Dakatar da Betta Edu da Tsare Sadiyar Umar Farouk

  • Hukumar EFCC ta na binciken game da kudin da ake zargin an sace a ma’aikatar jin-kai ta kasa
  • A sakamakon binciken, an tono N30bn da ake tunanin an wawura daga cikin wasu N37,170, 855,753.44
  • Sadiya Umar-Farouk da magajiyarta watau Betta Edu suna cikin wadanda jami’an EFCC suka taso gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta sanar da cewa an gano N30bn da ake zargin an karkatar a ma’aikatar tarayya.

Wadannan kudi suna cikin N37,170, 855,753.44 da ake zargin an yi awon gaba da su daga ma’aikatar jin kai, Punch ta kawo rahoton.

EFCC.
EFCC tana binciken Sadiya Umar-Farouk da Betta Edu Hoto: @Sadiya_farouq, @officialEFCC, @edu_betta
Asali: Twitter

Sadiya Umar-Farouk v EFCC

Ana zargin an tafka badakalar kudin ne a lokacin Sadiya Umar-Farouk ta na rike da minista. Tsohuwar jami'ar ta karyata zargin nan.

Kara karanta wannan

Dukiyar talakawa: EFCC ta yi nasarar ƙwato zunzurutun kuɗi sama da N70bn cikin kwana 100

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari ya kafa ma’aikatar jin kai, yaki da talauci da bada agajin gaggawa, Sadiya Umar-Farouk ta fara zama minista.

EFCC tana binciken 'badakalar' N37bn

Ana da labarin yadda aka cire N37,170,855,753.44 daga asusun gwamnatin tarayya, aka tura zuwa akawun 38 a bankunan ‘yan kasuwa.

Zargin da ake yi shi ne wani ‘dan kwangila, James Okwete yana da alaka da wadannan asusu.

Rahoton ya ce EFCC tayi nasarar garkame asusun na Umar-Farouq da Okwete da ke bankuna yayin da bincike yake cigaba da gudana.

Wani jami’in EFCC ya ce ana binciken tsohuwar Ministar da ‘dan kwangilar, kuma a duk rana su na amsa tambayoyi a ofishin hukumar.

Lambar Betta Edu ta fito a EFCC

Majiya daga hukumar ta EFCC sun shaida an bankado badakalar N500m da ake zargin Betta Edu tana da hannu kafin a dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Ahmed Musa Ya Ba Super Eagles Sirrin Doke Kasar Angola a Gasar AFCON 2023

Bayan haka, hukumar ta tasa Betta Edu a gaba a kan zargin satar N17bn sannan ana binciken Halima Shehu game da cin N44bn a NSIPA.

Idan labarin ya tabbata, Dr. Edu tana cigaba da bada hadin-kai wajen binciken da ake yi. Kakakin EFCC bai ce uffan game da zancen ba.

Halima Shehu ta fada ragar EFCC

Ku na da labarin Halima Shehu ta shugabanci tsarin tallafawa marasa karfi na NSIPA kafin Mai girma Bola Tinubu ya dakatar da ita a 2023.

Bayan an kori Shehu ne sai aka kawo Akindele Egubwalo a matsayin shugaban riko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel