EFCC Ta Gano Kungiyar Addini Da Ke Taimakon ‘Yan Ta’adda

EFCC Ta Gano Kungiyar Addini Da Ke Taimakon ‘Yan Ta’adda

  • Ola Olukoyede ya ce akwai kungiyoyi da shugabannin addini dumu-dumu a harkar satar kudin jama’a
  • Shugaban hukumar EFCC ya tona asirin yadda ake amfani da sunan addini domin a wawuri dukiyar haram
  • Olukoyede ya yi bayanin nan ne da aka gayyato shi domin yin jawabi a wani taro da aka shirya a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban EFCC mai yaki da rashin gaskiya, Ola Olukoyede ya shaida cewa hukumarsa ta bankado asirin wata kungiyar addini.

A ranar Larabar nan, Punch ta rahoto Ola Olukoyede yana cewa sun gano kungiyar addinin da ke yi wa ‘yan ta’adda safarar kudi a Najeriya.

EFCC.
Shugabannin hukumar EFCC Hoto: PM News, thecable.ng
Asali: UGC

EFCC ta tona alakar 'yan ta'adda da masu addini

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Kano, Jigawa Ba Su Fama Da Matsalar 'Yan Bindiga: Shehu Sani Ya Magantu

Baya ga masu taimakawa miyagu wajen yawo da kudi, EFCC ta ce akwai kungiyar addinin da aka samu da bada kariya ga marasa gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken hukumar ya kai ga wasu kudi da ake zargin sato su aka yi, ko da bincike ya yi zurfi sai aka samu kudin a asusun kungiyar addinin.

Hukumar EFCC tayi taro a Abuja

Bayanan nan sun fito ne a lokacin da Olukayode ya gabatar da jawabi a cibiyar Shehu Yar’Adua wajen wani taron kwana guda da aka shirya.

Taken taron da aka shirya a garin Abuja shi ne matasa, addini da yaki da rashin gaskiya. Labarin nan ya zo a rahoton jaridar The Nation.

Olukayode ya ce an hana EFCC aiki

Ko da hukumar ta EFCC ta dage domin yin bincike a kan lamarin, sai aka aiko mata takarda inda aka umarci ta dakatar da wannan aiki.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

A nan shugaban hukumar ya fasa kwan yadda aka rika samun kungiyoyi, malamai, bangarori da cibiyoyin addinai da laifin satar dukiya.

"An samu wata kungiyar addini a kasar nan tana safarar kudi domin ‘yan ta’adda."
"Mun iya gano wasu kudin sata a kungiyoyin addini, kuma da muka tuntubi kungiyoyin addinan game da lamarin, muna bincike, sai ga umarnin dakatar mu daga gudanar da aikinmu."

- Olu Olukayode

'Yan siyasa masu addinin karya

Ana da labari Buba Galadima ya ce a siyasa, sun san na-kirki, bara-gurbi, na banza da manufukai masu ci da addini domin samun matsayi.

Injiniya Buba Galadima yake cewa yanzu masu kururuwan tikitin Muslim-Muslim a zaben 2023 ba su tsira da komai a gwamnatin APC ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel